Dalilin da yasa nake farinciki da binciken da EFCC ke yi min – Babachir David Lawal

Dalilin da yasa nake farinciki da binciken da EFCC ke yi min – Babachir David Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir David Lawal, ya ce yana farinciki da binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ke yiwa zargin da ake masa na almundahana.

Babachir ya bayyana hakan ne yayin wata hira mai tsawo da ya yi da gidan talabijin na Channels a wani shirin su mai suna “Hard Copy”.

Ina son hakan, a takaice ni da kai na naso EFCC ta binciki zargin da ake yi min domin tana da ma’aikata da kayan aiki da zata iya gano gaskiyar zargin da ake yi min,” a cewar Babachir.

Dalilin da yasa nake farinciki da binciken da EFCC ke yi min – Babachir David Lawal

Babachir David Lawal

Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige Babachir ne a ranar 30 ga watan Oktoba, 2017, biyo bayan zargin sa da bayar da aikin kwangilar yankan ciyawa a sansanin ‘yan gudun hijira ga kamfanin sa, laifin da ya saba da doka. Saidai Shugaba Buhari ya ce cire Babachir ba zai shafi alakar su ta zumunci ba.

DUBA WANNAN: Goron Sallah daga shugaba Buhari

Dangane da dangantakar sa da shugaba Buhari, Babachir ya ce, “shugaba Buhari tamkar dan uwa ne gare ni, saboda haka babu abinda zai shafi alakar mu don ya cire ni daga mukami.”

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagorancu kwamitin day a bayar da shawarar cire Babachir daga mmukamin sa bayan tabbatar da samun sad a laifin saba ka’ida a bayar da kwangilar waasu aiyuka a sansanin ‘yan gudun hijira.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel