Yanzu-yanzu: Makiyaya sun saki wani malamin kirista da wasu mutane 2 da suka kama

Yanzu-yanzu: Makiyaya sun saki wani malamin kirista da wasu mutane 2 da suka kama

- Rabon shan ruwan wasu mutane da masu garkuwa kama ya zo ciki har da malamin kirista

- An dai kame su ne tun a ranar Lahadin da ta gabata

- Amma ga mamakin masu tambaya, ko sisi ba'a biya ba haka nan kawai aka sake su

Wani malamin kirista mai suna Kayode Akande ya samu damar shaker iskar ‘yancin bayan sakin shi da wasu makiyaya su kayi tare da wasu mambobin cocinsa a jihar Osun.

Yanzu-yanzu: Makiyaya sun saki wani malamin kirista da wasu mutane 2 da suka kama

Yanzu-yanzu: Makiyaya sun saki wani malamin kirista da wasu mutane 2 da suka kama

Guda daga cikin malaman cocin ne ya shaida hakan ga wakilin jaridar Punch ta wayar salula a yau juma’a cewa, Bankole da kuma Omodunbi suma duk an sako su tare.

Ya ce “An sako malamin da mambobin cocin biyu ana zargin wadansu da ake kyautata zaton makiyaya ne, kuma sun sako su a jiya alhamis sannan sun sake su ne ba tare da wata cutarwa ba”.

KU KARANTA: Mutuwa mai yankan kauna: Hukumar shige da fice ta kasa tayi babban rashi

Majiyarmu dai ta tabbatar da cewa an kama mutanen ne tun a daren ranar Lahadi kuma an sake su ne ba tare da wata cutarwa ba.

Amma da aka tambaye shi nawa aka biya kudin fansa, majiyar ta bayyana cewa, ko sisi ba’a biya ba. Malamin ya roki masu garkuwar ne da su taimaka su sake su sannan yayi musu add’ua.

Majiyar ta bayyana “Cocinmu bata biya kudin fansa ba, kawai Ubangiji ne ya shiga lamarin aka sako su, sannan shi ma malamin yayiwa masu garkuwar addu’a”.

Sun aiko da takardar neman fansa, amma malamin ya roke su kuma da Ubangiji ya shiga lamarin sai suka tausaya suka sake su su ukun duka”.

Har ya zuwa yanzu kakakin ‘yan sanda na jihar ta Osun Folasade Odoro bai ce komi kan faruwar lamarinba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel