Yan sanda na cigaba da samun nasarar kama masu hannu a fashin Offa

Yan sanda na cigaba da samun nasarar kama masu hannu a fashin Offa

- Hukumar yan sanda ta sake kama wasu gungun mutane guda biyar wanda ake zargin suna da hannu a fashi da makamin da aka yi na garin Offa

- An kama mutane biyar din ne a kudu maso yammacin kasar nan, a yayin da hukumar take maida ragowar shugaban yan fashin yankin da suka aikata laifin

Wata sabuwa : 'Yan Sanda sun sake cafke mutane 5 da ake zargin suna da hannu a fashi-da-makamin Offa

Wata sabuwa : 'Yan Sanda sun sake cafke mutane 5 da ake zargin suna da hannu a fashi-da-makamin Offa

Sashin tattara bayan sirri na rundunar yan sanda ya sake kama mutane 5 da ake zargin suma suna da hannu a fashin da aka yi na garin Offa a ranar 5 ga watan Afrilun 2018.

Mutane 5 din an cafke su ne tare da taimakon shugaban yan fashi da makamin da yake hannun 'yan sanda, bayan maida shi kudu maso yammacin kasar nan, wanda hakan ya taimakawa jami'an tsaro wajen cafke wasu tare da bankaɗo wasu makamai wanda suke da alaƙa da fashin da ya auku a Bankin dake garin na Offa.

KU KARANTA: Gwamnati ta sanya takunkumin zirga-zirga da ababen hawa na tsawon sa'o'i 12 a Jihar Yobe

Idan za a iya tunawa korarren Jami'in dan sanda Michael Adikwu shi ne uwa-uba wajen haɗo kan wasu wanda suka taimakawa wajen aikata wancan fashi-da-makami a garin na Offa. Adikwu ya taimaka wajen kamo wasu tare da kama wasu makamai.

Idan ba a manta ba Legit.ng ta rahoto cewa, hukumar ta yan sanda ta gayyaci Shugaban majalisar dattijai Dr. Abubakar Bukola Saraki domin ya zo ya amsa tambayoyi game da iƙirarin cewa yana da hannu a cikin fashin da aka yi.

Kakakin hukumar 'yan sanda ta kasa baki daya Jimoh Moshood, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi 3 ga watan Yuli 2018 a birnin tarayya, a yayin da aka gurfanar da mutane 22 da ake zargin suna da hannu a fashin na garin Offa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel