Mun daura Damarar magance matsalar rashin aikin yi - Osinbajo

Mun daura Damarar magance matsalar rashin aikin yi - Osinbajo

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya sake tabbatar wa da 'yan Najeriya jajircewa gwamnatin tarayya wajen kwazon ta na magance matsalolin rashin aikin yi a fadin kasar nan.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da kungiyar matasa, 'yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki na bangarorin kasuwanci, noma da kuma fasahar sadarwa yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai jihar Edo.

Osinbajo ya jaddada goyon baya na gwamnatin wajen tallafawa masu kananan sana'o'i ta hanyar inganta ma su hannun jari da kuma shawarwari ga cibiyoyi na kanana da matsakaitan sana'o'i.

Ya kuma jaddada yadda shirye-shiryen nan na gwamnatin tarayya ke da muhimmanci ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na bayar da makamar aikin yi ga matasa 200, 000 yayin da ake sa ran adadin su zai kai 300, 000 zuwa karshen watan Yuni.

Mun daura Damarar magance matsalar rashin aikin yi - Osinbajo

Mun daura Damarar magance matsalar rashin aikin yi - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar ya bayanin cewa, akwai matukar muhimmanci kasancewar su wajen tabbatar da sun magance matsalolin rashin aikin yi musamman a tsakankanin matasan kasar nan.

KARANTA KUMA: Wani 'Dan Majalisa ya zargi Kwankwasiyya da shirin tayar da Tarzoma cikin Jihar Kano yayin Bikin Sallah

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, mataimakin shugaban kasar ya bayyana wasu hanyoyi biyu na samar da aikin yi a kasar nan da suka hadar da ire-iren shirin N-Power da kuma bayar da hannayen jari domin matasa su kafa kansu da sana'o'i tare da samar da masana'antu gami da koyar da sana'o'in hannu domin dogaro da kai.

A nasa bangaren, tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole, ya yabawa kwazon da gwamnatin tarayya ke yi wajen magance matsalolin rashin aikin yi musamman mataimakin shugaban kasa da ya karbi wannan ragama ta tabbatar da hakan a gwamnatin su da shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel