Baya ta haihu: Kotu ta umarci gwamnatin Adamawa ta biya wasu korarrun malaman makaranta 659 miliyan N660m

Baya ta haihu: Kotu ta umarci gwamnatin Adamawa ta biya wasu korarrun malaman makaranta 659 miliyan N660m

- Kotun ma'aikata ta ƙasa (NICN) ta umarci gwamnatin jihar Adamawa a jiya Alhamis da ta biya wasu malaman makaranta 659 da ta kora Naira miliyan N660m

- Ma'aikatan dai sun shigar da karar bayan daukarsu aiki da akayi sannan kuma aka hana su albashin sama da shekaru biyu

Baya ta haihu: Kotu ta umarci gwamnatin Adamawa ta biya wasu korarrun malaman makaranta 659 miliyan N660m

Baya ta haihu: Kotu ta umarci gwamnatin Adamawa ta biya wasu korarrun malaman makaranta 659 miliyan N660m

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya dai rawaito a ranar 11 ga watan Agusta 2015 cewa, malaman sun yi ƙarar gwamnatin Adamawan da ma'aikatar ilimi da hukumar kula da ilimin makarantun gaba da sakandire da kuma kwamishinan shari'a na jihar,suna roƙon kotun da ta tabbatar da sahihancin ɗaukarsu aiki kasancewar har sun shafe watanni 29 suna koyarwa.

A soboda haka bayan yin aikin watanni 29 sun cancanta da a biya su albashi da sauran haƙƙinsu na sallama daga aikida ya kai N638.9m.

Da yake zartar da hukuncin, mai shari'a Juustice Nelson Ogbuanya na kotun NICN, ya ce gwamnatin jihar ta gaza gamsar da kotun korar ma'aikatan da take iƙirari.

Bisa hakan malaman makarantar sun cigaba da kasancewa ma'aikatan jihar tun daga watan Agustan 2012 har ya zuwa yau.

KU KARANTA: Yan sanda na cigaba da samuna nasarar kama masu hannu a fashin Offa Saboda haka ne alƙalin ya umarci gwamnatin jihar Adamawan da ta biya su albashinsu na watanni 29 da suka shafw suna aiki nan da makonni biyu masu zuwa.

Sannan ta sake biyan ƙarin wasu miliyan N22m a matsayin kudin tararrabi da kailular rashin aiki da gwamnatin ta jefa su ba tare da albashi ba. Bayan yanke hukuncin, lauyan gwamnatin jihar Adamawan Mr Urbanus Jonathan, ya ce yayi matuƙar mamaki da kaɗuwa da hukuncin. Kuma zai koma ya nazarci yadda aka yanke hukunci kafin sanin matakin da zasu ɗauka.

Shi kuwa lauyan masu ƙarar (Malaman) Abubakar Babakano, cewa yayi wannan hukunci abu ne da ya dace kuma hakan na nuna martabar sashin shari'a a idon maras galihu na farfaɗowa. Sannaya bayyana cewa tunda an yanke hukunci, yanzu zasu jira don ganin an aiwatar da umarnin kotun.

Malaman dai gwamnatin jihar ce ta ɗauke su aiki tun a lokacin tsohon gwamna Murtala Nyako a shekara ta 2012. Bayan ɗaukarsu aikin sai aka rarrabash zuwa wuraren aikinsu gami da basu lambobin kama aiki, kuma sun karɓi albashi har na tsawon watanni shida.

Amma kwatsam sai gwamnatin ta dakatar da biyansu albashinsu bisa bujjar wai su ɗin ba kwararrun malamai ba ne kasancewar ba su da Digiri ko wata shaidar ilimin koyarwa ta ƙasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel