An bukaci kotu ta umurci EFCC ta fara gudanar da bincike a kan Oshiomole

An bukaci kotu ta umurci EFCC ta fara gudanar da bincike a kan Oshiomole

- Wani Bishof Osadolor Ochei, mai gwagwarmayar yaki da rashawa ya bukaci kotun tarayya ta bukaci EFCC ta fara gudanar da bincike a kan Kwamared Adams Oshiomole

- Bishop din ya na zargin Oshiomole da wawure kudaden al'umma lokacin da yake gwamna a jihar Edo

- Ya ce ya taba shigar da korafi a kan Oshiomole a 2016 amma EFCC bata dauki mataki a wannan lokacin ba

Wani malamin addinin kirista Bishof Osadolor mai gwagwarmayar yaki da rashawa ya bukaci kotun tarayya ta bukaci yaki da rashawa na kasa EFCC ta fara gudanar da bincike a kan tsohon gwamnan jihar Edo kuma dan takatar ciyaman din jam'iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshiomole.

Toh fah! An bukaci kotu ta umurci EFCC ta fara bincike a kan Oshiomole

Toh fah! An bukaci kotu ta umurci EFCC ta fara bincike a kan Oshiomole

KU KARANTA: A karo na farko, mahaifiyar Shekau tayi magana a kan Boko Haram

Bishof din ya shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/628/2018 ne a ranar Laraba 14 ga watan Yuni, wannan ya biyo bayan karar da ya fara shigarwa a kan Oshiomole tun a ranar 28 ga watan Oktoban shekarar 2016 inda ya ke zargin Oshiomole da wawure kudin al'umma yayin da ya ke gwamna.

Legit.ng ta gano cewa Bishof din yana bukatar kotu ta bayar da umurni ga hukumar EFCC ne saboda zargin da ya ke yiwa tsohon gwamnan wanda kuma kudin tsarin mulki ta bashi damar gabatar da irin wannan korafin a kan tsohon gwamnan.

Kazalika, Bishof din ya yi ikirarin cewa hukumar EFCC bata dauki wani mataki a kan korafin da ya shigar a baya ba duk da cewa akwai alamun rashawa da cin hanci ya ratsa yan Najeriya sosai.

A cewar Bishof din, Oshiomole ya sace kudaden al'ummar jihar Edo ya azurta kansa dashi a yayin da ya ke gwamnan jihar.

A halin yanzu, babban alkalin babban kotun Abuja, Justice Abdul Kafarati bata saka ranar da za'a fara sauraran karar da Bishof din ya shigar ba.

A wata rahoton kuma, Legit.ng ta ruwaito cewa Adams Oshiomole ya ce ya kamata a kama tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a aike da shi gidan yari muddin an same shi da aikata wasu laifuka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel