Dattijan kuduncin Najeriya sun ce Buhari ya tsige shugaban hukumar INEC

Dattijan kuduncin Najeriya sun ce Buhari ya tsige shugaban hukumar INEC

Wasu dattijan Najeriya a makon da ya gabata sun bukacin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da ya gaggauta tsige shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) mai suna Farfesa Mahmoud Yakubu.

Wadanda suka yi kiran dai su ne Air Commodore Nkanga Idongesit da Chief Edwin Clark daga kudu maso kudancin Najeriya, Chief Ayo Adebanjo daga kudu maso yammacin Najeriya, Chief Chukwuemeka Ezeife daga kudu maso gabashin Najeriya, da kuma Air Commodore Dan Suleiman daga Arewa ta tsakiyar Najeriya.

Dattijan kuduncin Najeriya sun ce Buhari ya tsige shugaban hukumar INEC

Dattijan kuduncin Najeriya sun ce Buhari ya tsige shugaban hukumar INEC

KU KARANTA: Tsaffin gwamnoni 4 da aka taba daurewa a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa sai dai tuni wata kungiya mai zaman kanta a Najeriyar mai rajin tabbatar da mulkin demokradiyya mai suna Independent Service Delivery Monitoring Group (ISDMG) ta yi fata-fata da dattijan inda ta ce masu kishin kasa.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci karin hakuri daga 'yan Najeriya domin a cewar sa an jefa kasar cikin mawuyacin hali kafin zuwan sa kuma daman indai za'a yi gyara to dole ne sai an wahala.

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar barka da Sallah da ya aikewa 'yan Najeriya dauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman ta fannin harkokin yada labarai, Garba Shehu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel