Dalilin da yasa na fice daga PDP na koma Labour Party - Mimiko

Dalilin da yasa na fice daga PDP na koma Labour Party - Mimiko

Tsohon gwamna Jihar Ondo, Olusegun Mimiko ya fice daga PDP koma jam'iyyar da ya baro a baya wato Labour Party a wato taro da akayi a kauyen su a jihar Ondo.

A dai ranar Laraba da ta gabata ne ya rubuta wasika ga shugaban jam'iyyar PDP inda ya sanar dashi cewa zai fice daga jam'iyyar duk da cewa bai bayyana dalilinsa na fita a cikin wasikar ba.

KU KARANTA: A karo na farko, mahaifiyar Shekau tayi magana a kan Boko Haram

A jawabin da ya yi ranar Alhamis a Civic Centre a garin Ondo, Mr Mimiko ya shaidawa al'umma cewa ya baro PDP ne saboda yana son ya koma jam'iyyar da ke akidar da ta dace da bukatun talakawan Najeriya a yanzu.

Dalilin da yasa na fice daga PDP na koma Labour Party - Mimiko

Dalilin da yasa na fice daga PDP na koma Labour Party - Mimiko

Tsohon gwamnan bai nuna wata damuwa ba duk da cewa akwai wata bangare a jam'iyyar Labour da ke nuna rashin jin dadinsu da dawowa jam'iyyar ta Labour da ya yi.

A cewarsa, dukkan sauran jam'iyyun Najeriya har ma da PDP suna amfani da akidu ne wanda basu dace da bukatun yan Najeriya ba yanzu.

Mimiko ya lashe zaben gwamna har sau biyu, da farko a karkashin jam'iyyar PDP, sai karo na biyun a karkashin jam'iyyar Labour kafin daga baya ya sauya sheka zuwa PDP kuma ya zama ciyaman na kungiyar gwamnonin PDP.

Tsohon gwamnan ya bayyana niyyarsa ta dawowa jam'iyyar Labour cikin kalamai masu dadi a yayin da ya ke jawabinsa na komawa jam'iyyarsa ta Labour.

Yana kyautata zaton komawarsa sai bashi damar yiwa yan Najeriya hidima a karkashin jam'iyyar da ke da manufofin biyan bukatun al'ummar Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel