To fa: An maka wani matashi dan shekara 25 kotu bisa laifin tabawa matar aure nono a Najeriya

To fa: An maka wani matashi dan shekara 25 kotu bisa laifin tabawa matar aure nono a Najeriya

Yanzu haka dai wata kotun Majistare dake zaman ta a garin Legas ta soma sauraron karar da aka shigar gaban ta ta wani matashi dan shekara 25 da wata matar aure mai suna Faith Ijiogbe ta ce ya taba mata nono.

Kamar dai yadda muka samu, matashin mai suna Kabiru Saka ya taba nonon matar auren ne lokacin da ta fasa masa kwalebanin lemunan sa da ya siya a hannun matar.

Ta fa: An maka wani matashi dan shekara 25 kotu bisa laifin tabawa matar aure nono a Najeriya

Ta fa: An maka wani matashi dan shekara 25 kotu bisa laifin tabawa matar aure nono a Najeriya
Source: UGC

KU KARANTA: Kotun tarayya ta makkawa gwamnati Naira biliyan 2.2 ta wani tsohon hafsan soja

Legit.ng ta samu cewa matar ta ce a nan ne fa sai wani dan rikici ya so ya barke a tsakanin su inda shi ya nuna bai yadda ba har ya kaiga taba mata nono.

Alkalin kotun dai ya bayar da belin wanda ake kara kan kudi Naira dubu 100 tare da dage shari'ar zuwa 23 ga watan Yuli mai kamawa.

A wani labarin kuma, Wasu dattijan Najeriya a makon da ya gabata sun bukacin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da ya gaggauta tsige shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) mai suna Farfesa Mahmoud Yakubu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel