Wani Farfesa ya gamu da Ajali cikin Ofishin sa a wata Jami'ar Jihar Bayelsa

Wani Farfesa ya gamu da Ajali cikin Ofishin sa a wata Jami'ar Jihar Bayelsa

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, an yi kacibus da gawar wani babban Malami na jami'ar Afirka dake garin Toru-Orua a jihar Bayelsa, Farfesa Prince Efere.

Rahotanni sun bayyana cewa, abokan aiki wannan babban Malami da ya karantu a kasar Birtaniya sun yi kacibus ne da gawar sa ya yayin da bai halartar wani taro na ganawa da suka shirya gudanarwa a jami'ar.

Abokan aikin na sa da suka tabbatar da wannan rahoto mai tattare da bakin ciki sun bayyana cewa, sun riski gawar sa ne tare da kansa jingine akan Teburin ofishin sa.

Wani Farfesa ya gamu da Ajali cikin Ofishin sa a wata Jami'ar Jihar Bayelsa

Wani Farfesa ya gamu da Ajali cikin Ofishin sa a wata Jami'ar Jihar Bayelsa

Legit.ng ta fahimci cewa kafin mutuwar Efere, shine shugaban cibiyar ilimi ta yawon bude idanu da shakatawa da gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, ya nada wadda aka kafa ta tun a shekarar 2013 da ta gabata.

KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga sun Kashe wani Mamba na Jam'iyyar APC a jihar Ekiti

A shekarar 2017 da ta gabata ne aka nada marigayi Efere wanda yake da shedar kammala karutun Digiri na uku har a fannukan nazari kashi biyu shugaban cibiyar kulawa da kiwon lafiya na reshen sabuwar jami'ar Afrika dake garin Toru-Orua a jihar Bayelsa.

Hakazalika, Farfesan ya kasance mamba cikin kwamitin hada kawunan al'umma na jihar kuma shugaban cibiyar ilimi ta kasar Birtaniya watau British Education Network.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel