Wani 'Dan Majalisa ya zargi Kwankwasiyya da shirin tayar da Tarzoma cikin Jihar Kano yayin Bikin Sallah

Wani 'Dan Majalisa ya zargi Kwankwasiyya da shirin tayar da Tarzoma cikin Jihar Kano yayin Bikin Sallah

Babban jagora na Majalisar Dokoki ta jihar Kano, Honarabul Baffa Babba Dan Agundi, ya yi zargin cewa akwai wani tuggu da kungiyar Kwankwasiyya take kullawa na tayar da tarzoma cikin Jihar Kano yayin gudanar da shagulgulan Sallah.

Dan Agundi wanda ke wakiltar mazabar Birnin Kano cikin wata rubutacciyar wasika ya sanad da Sufeto Janar na 'yan Sanda Ibrahim Idris, tare da sauran hukumomin tsaro akan su kawo dauki dangane da wannan hargitsi da tarzoma da kungiyar Kwankwasiyya ke shirin tayar wa cikin jihar.

Cikin rubutacciyar wasikar, Babba Dan Agundi ya zargi Kungiyar Kwankwasiyya da kuma jagoranta, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso akan tayar da tarzoma gami da hargitsi cikin jihar musamman a kewayen fadar Sarkin Kano yayin gudanar da Shagulgulan bikin Sallah.

Legit.ng ta fahimci cewa, Dan Agundi ya aika wannan wasika zuwa ga gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Babban mai bayar da shawara akan harkokin tsaro na Kasa, Babagana Mongunu, Sarkin Kano, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, Kakakin Majalisar Dokoki na jihar, Honarabul Abdullahi Yusuf Attah da kuma Shugaban hukumar Civil Defense na jihar.

Wani 'Dan Majalisa ya zargi Kwankwasiyya da shirin tayar da Tarzoma cikin Jihar Kano yayin Bikin Sallah

Wani 'Dan Majalisa ya zargi Kwankwasiyya da shirin tayar da Tarzoma cikin Jihar Kano yayin Bikin Sallah

Dan Agundi ya kuma zargi tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Rabi'u Bichi, tsohon shugaban ma'aikata kuma Kwamishinan Ruwa na Gwamnatin Kwankwaso, Dakta Haruna Adamu Dangwani wajen kulla tuggun kawo hargitsi da tarzoma a jihar Kano.

KARANTA KUMA: Fashin Offa: Hukumar 'Yan sanda ta sake cafke wasu da ake zargi a jihohin Kogi da Oyo tare da Muggan Makamai

Wasikar ta kuma bayyana yadda masoya da kuma magoya bayan Kwankwaso daga jihohin Katsina, Jigawa, Bauchi da kuma Kano za su yi dandanzo a harabar Fadar Sarkin Kano domin kawo hargitsi gami da assasa zagon kasa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummar Jihar Kano.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Kamfanonin Jiragen Sama na Najeriya sun sayar da Tikitin Jigilar Al'umma na kimanin Naira Biliyan 505 a shekarar 2017 da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel