"Sai in kashe ka, na kashe banza" - Inji wani jami'an 'yan sandan Najeriya

"Sai in kashe ka, na kashe banza" - Inji wani jami'an 'yan sandan Najeriya

Wani dan Najeriya ma'abocin anfani da kafar sadarwar zamani ta Tuwita ya kwarmata yadda yace wani jami'in 'yan sandan Najeriya dake aiki da rundunar tabbatar da hana munanan laifuka da kuma fashi da makami ta Special Anti-Robbery Squad (SARS) yace zai iya kashe shi kuma 'ya kashe banza'.

Kamar dai yadda muka samu, shi dai matashin mai suna Andrew Solomon ya nuna takaicin sa ne game da yadda yace jami'an rundunar 'yan sanda na Special Anti-Robbery Squad (SARS) suke cin zarafin al'ummar kasa da suna tabbatar da tsaro.

"Sai in kashe ka, na kashe banza" - Inji wani jami'an 'yan sandan Najeriya

"Sai in kashe ka, na kashe banza" - Inji wani jami'an 'yan sandan Najeriya

KU KARANTA: Bikin Sallah: Za'a zuba yan sanda 3,500 a jihar shugaban kasa

Legit.ng ta samu haka zalika cewa Andrew Solomon ya fallasa jami'in dan sandan da yace sunan sa John ta hanyar wallafa sunan sa a yanar gizo.

A wani labarin kuma, Mahukunta a kotun tabbatar da da'ar ma'aikata ta gwamnatin tarayya watau Code of Conduct Tribunal (CCT) ta fito ta karyata batun da ke yawo na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mai shari'a Adebukola Banjoko a matsayin shugabar ta.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in hulda da jama'a na hukumar kotun Malam Ibraheem Alhassan inda ya bayyana cewa har yanzu Mai shari'a Danladi Yakubu Umar ne shugaban alkalan kotun.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel