Kotun tabbatar da da'a tayi karin haske game nadin Mai shari'a Banjoko a matsayin shugaba

Kotun tabbatar da da'a tayi karin haske game nadin Mai shari'a Banjoko a matsayin shugaba

Mahukunta a kotun tabbatar da da'ar ma'aikata ta gwamnatin tarayya watau Code of Conduct Tribunal (CCT) ta fito ta karyata batun da ke yawo na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mai shari'a Adebukola Banjoko a matsayin shugabar ta.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in hulda da jama'a na hukumar kotun Malam Ibraheem Alhassan inda ya bayyana cewa har yanzu Mai shari'a Danladi Yakubu Umar ne shugaban alkalan kotun.

Kotun tabbatar da da'a tayi karin haske game nadin Mai shari'a Banjoko a matsayin shugaba

Kotun tabbatar da da'a tayi karin haske game nadin Mai shari'a Banjoko a matsayin shugaba

KU KARANTA: Tsaffin gwamnoni 4 a Najeriya da aka taba kullewa

Legit.ng ta samu cewa a baya dai jita-jita sun yi ta yawo a kafafen sadarwa musamman na zamani game da cewa wai an canza shugaban hukumar da babbar Mai shari'a Adebukola Banjoko biyo bayan hukuncin daurin shekaru 14 da ta yanke wa tsaffin gwamnonin Najeriya biyu.

A wani labarin kuma, Wani dan Najeriya ma'abocin anfani da kafar sadarwar zamani ta Tuwita ya kwarmata yadda yace wani jami'in 'yan sandan Najeriya dake aiki da rundunar tabbatar da hana munanan laifuka da kuma fashi da makami ta Special Anti-Robbery Squad (SARS) yace zai iya kashe shi kuma 'ya kashe banza'.

Kamar dai yadda muka samu, shi dai matashin mai suna Andrew Solomon ya nuna takaicin sa ne game da yadda yace jami'an rundunar 'yan sanda na Special Anti-Robbery Squad (SARS) suke cin zarafin al'ummar kasa da suna tabbatar da tsaro.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel