Kamfanonin Jiragen sama na Najeriya sun sayar da Tikiti na N505bn a shekarar 2017

Kamfanonin Jiragen sama na Najeriya sun sayar da Tikiti na N505bn a shekarar 2017

Hukumar kula da harkokin jiragen sama ta Najeriya NCAA (Nigerian Civil Aviation Authority) a ranar Alhamis din da ta gabata ta bayyana cewa, kamfonin jiragen sama na kasar nan sun sayar da tikiti na kimanin Naira Biliyan 505.6 a shekarar 2017 da ta gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, hukumar ta yi wannan fashin baki ne dangane da adadin tikitin da ta sayar na jigalar al'umma a cikin gida da kuma wajen kasar nan ta Najeriya.

Shugaban wannan hukuma Kaftin Mukhtar Usman, shine ya bayyana hakan yayin wani taron kasuwanci akan harkokin jiragen sama da aka gudanar a jihar Legas.

Legit.ng ta fahimci cewa, an gudanar da wannan taro ne dangane da binciken harkokin tsaro da na kasuwancin hukumomin jiragen sama cikin shekaru hudun da suka gabata.

Usman wanda shugaban hukumai mai kula da harkokin korafe-korafen kwastomomi, Kaftin Adamu Abdullahi, ya bayyana cewa an samu habakar sayar da tikitin da kaso 14.2 cikin 100 da adadin kudin yake Naira Biliyan 82.7 idan aka kwatanta da na Naira Biliyan 422.4 da aka sayar a shekarar 2016 da ta gabata.

Kamfanonin Jiragen sama na Najeriya sun sayar da Tikiti na N505bn a shekarar 2017

Kamfanonin Jiragen sama na Najeriya sun sayar da Tikiti na N505bn a shekarar 2017

A cewar sa, kamfanonin jiragen guda takwas na masu jigila a cikin gida sun sayar da tikiti na kimanin Naira Biliyan 93.6 yayin da masu jigalar kasashen ketare suka sayar da na kimanin Naira Biliyan 411.6 a shekarar da ta gabata.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya Shugaba Buhari zai lashe Zaben 2019 - Keyamo

Ya kara da cewa, adadin kudin tikitin zai kasance sama da hakan ba don rufe filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja har na tsawon makonni shida domin bawa gwamnati dama ta gudanar da muhimman gyara a cikin sa.

Hakazalika akwai nakasun samun doriya akan wannan adadin kudi sakamakon rufe filin jirgin sama na Birnin Maiduguri a sanadiyar matsalolin tsaro da jihar Borno ta fuskanta wancan lokuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel