Wasu lauyoyi sun yunkuro domin fitar da Nyame daga gidan yari

Wasu lauyoyi sun yunkuro domin fitar da Nyame daga gidan yari

Wasu manyan lauyoyi sunyi korafi a kan hukumar yaki da rashawa EFCC game da hukuncin da aka zartas wa tsohon gwamnan Jihar Taraba Jolly Nyame na shekaru 14 ba tare da zabin biyan tara ba.

Jagoran lauyoyin Mr. Aiden Anthony da Mr. Pwamaddi Maboyofe Shagnah sun aike da takardar kokensu ga shugaba Buhari da Ciyaman din kwamitin yaki da rashawa da Attorney Janar na kasa da Sakataren hukumar kare hakkin dan-adam da wasu kafafen yadda labarai inda suka ce akwai tangarda a hanyoyin da aka bi wajen zartas da hukuncin.

KU KARANTA: Ba zan iya tabbatar da nagartar hadiman Buhari ba - Keyamo

Wasu lauyoyi sun yunkuro domin fitar da Nyame daga gidan yari

Wasu lauyoyi sun yunkuro domin fitar da Nyame daga gidan yari

"Tabbas kowa na iya ganin cewa masu bincike a kan tsohon gwamnan sunyi katsalandan cikin shari'ar."

A cikin takardan koken da suka shigar, lauyoyin sunyi ikirarin cewa hukumar EFCC ta ki hukunta wasu manya-manyan jami'an gwamnatin Jihar Taraba da su kayi aiki tare da tsohon gwamnan.

Sun ce akwai bukatar a sake waiwayar shari'ar don a binciko wadanda suka taimakawa tsohon gwamnan wajen aikata laifukan na almundahana da kudin al'umma da cin amana.

Masu shigar da karar sunyi mamakin yadda hukumar EFCC ta kyale tsohon kwamishinan kudi na jihar Taraba da sauran jami'an gwamnatin da ake zargi da hannu cikin satar kudaden mutanen Jihar Taraba.

Har ila yau, lauyoyin suna bukatar hukuma ta tabbatar an hukunta wadanda suka gudanar da bincike a kan tsohon gwamnan saboda yadda suka kawar da kai ga sauran wadanda suka aikata laifi tare da gwamnan.

Sunyi kira ga hukumar EFCC ta dubi wannan koken nasu da gagawa tare da yin barazanar gurfanar da hukumar a kotu muddin suka ki gudanar da bincike a kan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel