'Yan Bindiga sun Kashe wani Mamba na Jam'iyyar APC a jihar Ekiti

'Yan Bindiga sun Kashe wani Mamba na Jam'iyyar APC a jihar Ekiti

A ranar Larabar da ta gabata ne wasu 'yan Bindiga suka salwantar da rayuwar wani Mamba na jam'iyyar APC a Jihar Ekiti, William Ayegoro.

Wani Mashaidin wannan Mugun gani ya bayyana cewa, maharan hayen akan baburin su na hawa sun diga dalmar harsashi na Bindiga har cikin kwakwalwar Ayegoro a kan hanyar Igbehin dake unguwar Atikankan a cikin birnin na Ekiti.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, an garzaya da wannan mutumi rai a hannun Mai Duka zuwa asibitin koyarwa na jami'ar jihar Ekiti dake babban birni na Ado-Ekiti inda likitoci suka yi iyaka bakin kokarin su wajen ceton ransa.

'Yan Bindiga sun Kashe wani Mamba na Jam'iyyar APC a jihar Ekiti

'Yan Bindiga sun Kashe wani Mamba na Jam'iyyar APC a jihar Ekiti

Rahotanni sun bayyana cewa, an garzaya da Ayegoro zuwa asibitin yayin da tuni ya fice daga hayyacin sa sakamakon rasa jini da ya yi inda ajali ya cimma sa a safiyar ranar yau ta Alhamis.

KARANTA KUMA: Kada ku zabi bangare a zaben 2019 - Birtaniya ta Gargadi Hukumar EFCC

Legit.ng ta fahimci cewa, maharan bayan harbe wannan mamba na jam'iyyar ta APC sun kuma arce cikin gaggawa daga harabar da suka aikata wannan aika-aika.

Sai dai a yayin fitar da wannan labari, Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Mista Celeb Ikechukwu ya bayyana cewa, har yanzu ba ya da wata masaniya dangane da afkuwar harin.

Mista Ikechukwwu ya kara da cewa, hukumar za ta dauki matakin da ya dace da zarar ta tabbatar da afkuwar harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel