Da dumin sa: ‘Yan sanda sun shammaci wasu masu garkuwa da mutane, sun bindige 3 daga cikin su

Da dumin sa: ‘Yan sanda sun shammaci wasu masu garkuwa da mutane, sun bindige 3 daga cikin su

A yau, Alhamis, hukumar ‘yan sanda a jihar Taraba ta sanar da cewar ta kasha wasu masu garkuwa da mutane uku (3) da suka dade suna addabar mazauna yankin kananan hukumomin Bali da Takum.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Mista David Akinremi, ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da aka raba ga manema labarai a Jalingo, babban birni jihar Taraba.

Da dumin sa: ‘Yan sanda sun shammaci wasu masu garkuwa da mutane, sun bindige 3 daga cikin su

‘Yan sandan Najeriya

Akinremi ya ce jami’an ‘yan sanda na ofishin Bali suka shammaci masu garkuwa da mutanen har maboyar su bayan samun bayanan sirri tare da bayyana cewar jami’an sun kai samame maboyar masu garkuwar ne a jiya, Laraba, kuma nan take suka harbe uku (3) daga cikin su.

DUBA WANNAN: Dakarun soji sun kubutar da wasu mutane 8 da masu garkuwa suka sace a Kaduna(Hoto)

Masu garkuwar sun dade suna tayar da hankalin mutanen dake yankin Bali da Takum kuma sun saci mutane da dama. Saidai sa’ar su ta kare yayin da jami’an mu suka shammace su har maboyar su, kuma an yi nasarar kasha uku daga cikin su yayin da ragowar suka tsere duk da sun samu raunukan harbi da bindiga,” a cewar kwamishina Akinremi.

Kazalika, kwamishinan y ace sun samu wasu bindigogi da alburusai a maboyar masu garkuwar da kuma wasu kayayayaki da ake zargin na mutanen da suka yi garkuwa das u ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel