Wani kwandasta zai shafe kwanaki 90 a kurkuku saboda lakaɗawa wata mata duka

Wani kwandasta zai shafe kwanaki 90 a kurkuku saboda lakaɗawa wata mata duka

- Saurin hannu ya kai wami matashi ya baro a jihar Legas

- Matashin ya nannaushi matar ne kawai don sunyi cacar baki

- Bayan gurfanar da shi gaban kuliya ya amsa laifinsa ba tare da wani ja'inja ba

Wata kotun Majistire dake zamanta a Ikeja a jihar Legas ta yankewa wa matashi mai suna Faruk Yusuf hukuncin shafe kwanaki ɗari ba goma a gidan yarin kirkiri.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara Sufeto Aondohemba Koti ya shaidawa kotun cewa, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Jinairu a kasuwar Ojuwoye dake Mushin a nihar ta Legas.

Wani kwandasta zai shafe kwanaki 90 a kurkuku saboda lakaɗawa wata mata duka

Wani kwandasta zai shafe kwanaki 90 a kurkuku saboda lakaɗawa wata mata duka

Ya ce wanda ake ƙarar ya daki tare da naushin wata mata mai suna Oyindamola Omoniyi a bakinta bayan sun ɗan yi sa'insa.

KU KARANTA: Wani mutum mai dauke da cutar kanjamau ya yadda ta ga mata fiye da 200 da gangan

Koti ya ce wannan laifi ne da ya saɓawa sashi na 170 na kundin manyan laifuka na jihar ta Legas 2015.

Daga nan ne mai shari'a Mrs M.O Tanimola ta yanke masa hukuncin ne na zama a kurkukun har na watanni uku tare da kuma aiki mai tsanani bayan da ya amsa laifinsa.

Alkaliyar ta kuma bashi zaɓin biyan tarar Naira 10,000 bayan da ya nemi sassauci.

"A bisa wannan laifi, na yanke maka hukuncin watanni uku a gidan yari ko biyan tarar 10,000". Domin duk wani mai shirin aikata laifi irin wannan ya koyi darasi daga wurin naka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel