Zan sake neman takara a 2019 – Sanata Gemade

Zan sake neman takara a 2019 – Sanata Gemade

- Barnabas Gemade ya bayyana cewa zai sake tsayawa takarar dan majalisa a 2019

- Yace gagarumin rawar gani da nasarorin da ya samu shekaru bakwai da ya shafe a majalisar dattijai sun isa su kai sa ga nasara

- Ya kuma yi watsi da cewar anba da tikitin mazabarsa ga yankin Kwande

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Benue North East a majalisar dattawa, Barnabas Gemade ya bayyana cewa zai sake tsayawa takarar dan majalisa a zaben 2019 mai zuwa.

Sanata Barnabas wanda ya bayyana hakan Makurdi yace gagarumin rawar gani da nasarorin da ya samu shekaru bakwai da ya shafe a majalisar dattijai sun isa su kai sa ga nasara a zabe mai zuwa.

Zan sake neman takara a 2019 – Sanata Gemade

Zan sake neman takara a 2019 – Sanata Gemade

Shugaban kwamitin na ayyuka na majalisar ya kuma yi watsi da cewar anba da tikitin mazabarsa ga yankin Kwande.

A bangare guda, Sanata Shehu Sani mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasa yace ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba iyalan marigaji Janar Shehu Musa Yar’adua, Dr Beko Kuti, Chima Ubani, da na Ken Saror Wiwa hakuri.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta aika sammaci ga shugaban DSS na Kano cewa ya gurfana gabanta a ranar 13 ga watan Yuli

Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na twitter a ranar, Alhamis, 14 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel