Harin ta’addanci: An kashe mutane biyu a Masallaci yayin da suke Sallar Asubah

Harin ta’addanci: An kashe mutane biyu a Masallaci yayin da suke Sallar Asubah

Wani mutumi dan ta’dda ya hallaka mutane biyu a wani Masallaci dake kasar Afirka ta kudu a lokacin da suke gabatar da Sallar Asubahi a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuni, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan mutumi ya kai harin ne a Masallaci dake garin Malmesbery, gab da babban birnin Cape Town, sai dai jami’an Yansanda sun samu nasarar bindige shi a lokacin da yayi kansu da wukar.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Za’a fara kidayan adadin mutanen da jami’an Yansanda ke ci zarafinsu

Masallata ne suka yi kiran Yansandan a lokacin da mutumin yake ta’asarsa, inda ba tare da wata wata ba suka garzaya Masallacin, kamar yadda Kaakakin rundunar Yansandan yankin, Noloyiso Rwexana ya bayyana, inda yace a yanzu haka sun mika mutane biyu da ya sassara zuwa Asibiti.

Harin ta’addanci: An kashe mutane biyu a Masallaci yayin da suke Sallar Asubah

Masallacin

“Maharin wanda bai haura shekaru Talatin ba yana dauke ne da wata sharbebiyar wuka, inda duk kokarin da Yansanda suka yi na ganin ya mika wuya ya ci tura, har ma yayi yunkurin kai ma wani Dansanda hari, nan take muka bindige shi.” Inji Kaakaki.

Kungiyar Musulman kasar Afirka ta kudu sun bayyana kaduwarsu da wannan hari, musamman yadda ya faru a karshen watan Ramadan, inda suka yi gargadin bai kamata ayi saurin yin has ashen manufar wannan mutumi ba, amma sun bada tabbacin yin cikakken bincike.

Ko a watan Mayu da ta gabata wasu yan bindiga sun yi ma Limamin wani Masallaci yankan rago, tare da jefa nakiya cikin Masallacin da yake limanci, wanda hakan ya janyo gabara, sa’annan suka tsere a cikin mota.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel