Mun daure Nyame da Dariye – EFCC ta fadi wani tsohon gwamna da zata mayar da hankali kan sa

Mun daure Nyame da Dariye – EFCC ta fadi wani tsohon gwamna da zata mayar da hankali kan sa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana cewar bincike da take yiwa wasu jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar APC ya wanke ta daga zargin da wasu ke yi mata na zabar wadanda zata bincika.

Mai Magana da yawun hukumar, Mista Wilson Uwujaren, ya fadi haka a wani jawabi da EFCC ta fitar a jiya, Laraba, a Abuja.

Uwujaren na Magana ne a kan nasarar da EFCC tayi a kan tsofin gwamnonin jihar Taraba da Filato, Nyame da Dariye.

Yanzu masu sukar mu dole su ji kunya tunda duk mutanen da kotu ta aike gidan yari ‘yan jam’iyyar APC ne. An dauki lokaci mai tsawo ana shari’ar su, amma dukkan su sun koma jam’iyyar APC kafin a yanke masu hukunci,” a cewar Uwujaren.

Mun daure Nyame da Dariye – EFCC ta fadi wani tsohon gwamna da zata mayar da hankali kan sa

Jami'an EFCC

An zabi Dariye sanata a karkashin tutar jam’iyyar APC amma ya koma jam’iyyar APC ana tsaka da shari’ar sa amma hakan bai hana mu cigaba da shari’ar da muke yi da shi ba,” Uwujaren ya fada.

DUBA WANNAN: Ku daina katsalandan a aikin da ba naku ba - Kotu ta yiwa majalisa tuni a kan iyakar hurumin ta

Ya kara da cewa, “yanzu haka tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, na fuskantar tuhuma duk day a koma jam’iyyar APC kuma hakan bai hana mu cigaba da tuhumar sa a gaban kotu ba. Yanzu muna jiran hukuncin da kotu zata yanke a kan sa tunda mun gama gabatar da shaidun mu.”

Hukumar EFCC ta bukaci jama’a das u bat a goyon baya a yakin da take yi da cin hanci a Najeriya ba wai sukar ta a kan tana tuhumar wasu mutane ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel