Eid-el-Fitri: Rundunar yan sanda zata tsaurara matakan tsaro a masallatan Idi

Eid-el-Fitri: Rundunar yan sanda zata tsaurara matakan tsaro a masallatan Idi

Sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris, ya tura jami’an tsaro a dukkanin masallatan idi dake fadin kasar duk a kokarinsu na tsaurara matakan tsaro yayin bikin karamar sallah.

Shugaban yan sandan ya umurci dukkanin mataimakan shugaban yan sanda da kwamishinoni yan sanda na jiha da su tsaurara matakan tsaro sannan su tabbatar da an tura isassun jami’an tsaro masallatan idi da sauran guraren bikin a fadin kasa.

Kakakin rundunar, Jimoh Moshood wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da yayi a Abuja a ranar Laraba, yace hakan zai hada da wajajen wasanni, wuraren jama’a da wuraren gwamnati.

Eid-el-Fitri: Rundunar yan sanda zata tsaurara matakan tsaro a masallatan Idi

Eid-el-Fitri: Rundunar yan sanda zata tsaurara matakan tsaro a masallatan Idi

Ya kara da cewa an zuba yan rangaji a manyan titunan tarayya domin tabbatar da tsaron matafiya, inda yace an umarce su da su hankalta sosai yayinda suke gudanar da ayyukansu.

KU KARANTA KUMA: Shari’an Nyame da Dariye ya nuna cewa bama son kai - EFCC

A halin da ake ciki, Rundunar yan sandan Minna, jihar Niger sun kama wani matashi dan shekara 18 mai suna Shamsu Abubakar inda yake shiga irin ta mata yana damfarar maza.

An kama shi ne sanye cikin hijabi da zani, inda ya sha kwaliyya sannan yasa takalmi da jaka iri guda na mata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel