Motar ‘yan sanda tayi karo da ta sojoji a Abuja

Motar ‘yan sanda tayi karo da ta sojoji a Abuja

An samu afkuwar wani hatsari tsakanin wasu motocin jami’an tsaro guda biyu a kusa da tashar mota ta Jabi dake birnin tarayya, Abuja.

Lamarin ya faru ne jiya, Laraba, da rana da misalign karfe 3:30 na rana a kan titin Obafemi Awolowo dake Abuja. An samu cunkluson ababen hawa sakamakon afkuwar hatsarin.

Wakilin jaridar Daily Trust da ya ziyarci wurin da abin ya faru, ya bayyana cewar, wata bakar motar ‘yan sanda ce kirar Hilux mai lamba NPF 133D ta zo ta doki wata farar mota kirar Hilux mai lamba PF4563 ta abokan aikin su, jami’an tsaro.

Motar ‘yan sanda tayi karo da ta sojoji a Abuja

Motar ‘yan sanda tayi karo da ta sojoji a Abuja

Wani shaidar gani da ido, Ismaila Sadiq, ya bayyana cewar hatsarin ya faru ne a daidai lokacin da bakar Hilux din tayi kokarin kaucewa dukan wata karamar mota. Farar motar da aka doka na tsaye ne gefen titi.

Kazalika wata mata, Chioma Udoh, da lamarin ya faru a kan idonta t ace lamarin ya haddasa cunkuson ababen hawa na kimanin tsawon mintuna 45.

DUBA WANNAN: Ku daina katsalandan cikin aiyukan da ba naku ba - Kotu ta yiwa majalisa tuni a kan iyakar ikon ta

Ta kara da cewar, ‘yan sandan da sojojin sun hada kai wajen taimakawa domin ganin an samu saukin cunkuson ababen hawa da suka haddasa.

Jami’in ‘yan sanda na ofishin Utako, CSP Gbenle Jimoh, ya tabbatar da faruwar hatsarin tare da bayyana cewar motar da abun ya rutsa da ita ta ofishin su ce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel