Dalilin da ya sanya Shugaba Buhari zai lashe Zaben 2019 - Keyamo

Dalilin da ya sanya Shugaba Buhari zai lashe Zaben 2019 - Keyamo

Festus Keyamo, Kakakin kungiyar yakin neman zabe ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Ubangidan sa zai lashe zaben 2019 sakamakon akidar sa ta kafa al'adun siyasa daban-daban a kasar kafin ya bar Kujerar sa.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya bayyana Kakakin wanda ya kasance babban Lauya ne a Kasar nan ya bayar da shaidar hakan ne yayin ganawa da manema labarai da cewar al'ada da akidar kawo sauyi a kasar nan ta Shugaba Buhari ita kadai ce za ta tabbatar da nasarar sa a zaben 2019.

Yake cewa, Shugaba Buhari yana bukatar lokaci domin dabbaka wannan akida da al'adu a faggen siyasa da suka sha bam-ban da sauran gwamnatocin baya.

Dalilin da ya sanya Shugaba Buhari zai lashe Zaben 2019 - Keyamo

Dalilin da ya sanya Shugaba Buhari zai lashe Zaben 2019 - Keyamo

Keyamo ya kuma buga misali da mafi akasarin matasan kasar nan da tun tasowar su suka tarar da tsarin gwamnati na jam'iyyar PDP da ya kasance kan akidar amfani da kudi wajen biyan kowace bukata.

KARANTA KUMA: Makiyaya sun salwantar da Rayukan Mutane 5 a jihar Nasarawa

Ya ci gaba da cewa, sabanin jam'iyyar PDP shugaba Buhari ba ya da bukatar da kudin gwamnatin tarayya wajen sake samun nasara a zaben 2019, inda ya ce magoya bayan sa kadai za su sadaukar da dukiyoyin su wajen tabbatar da hakan.

Ya kara da cewa, akwai bukatar shugaba Buhari ya ƙarfafa yaki da cin hanci da rashawa tare da kawo karshen matsaloli tsaro inda kuma ya yi tir gami da Allah-wadai ga masu hasashen shugaba Buhari ke da alhakin daukar nauyin rikicin makiyaya a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel