Da naga bata taba saduwa da namiji ba banyi mata fyade ba - inji wani Direba ga kotu

Da naga bata taba saduwa da namiji ba banyi mata fyade ba - inji wani Direba ga kotu

- Wani direba mai suna Emmanuel Okorie ana zargin shi da yi wa kanwar makwancin shi fyade, inda ya musa zargin da hukumar yan sandan jihar Legas keyi mishi

- Wanda ake zargin dai yana gaban babban kotun jihar Legas ta Igbosere. A rana laraba dai ya musa cewa bai aikata laifin ba

Da naga bata taba saduwa da namiji ba banyi mata fyade ba - inji wani Direba ga kotu

Da naga bata taba saduwa da namiji ba banyi mata fyade ba - inji wani Direba ga kotu

Emmanuel Okorie, direban tanka da aka kai gaban alkali, ya musanta zargin inda yace duk da dai ya kaita daka da wayo, bai kai ga yi mata komai ba, domin ya shafa yaga bata tara wa da maza.

Okorie ya tabbatar a gaban mai shari'a Oluwatoyin Ipaye cewa "Na kyaleta ne a lokacin da na gano budurwa ce. Na saka hannuna a gaban ta, da na gane cewa budurwa ce, sai na kyaleta. Ban kusance ta ba saboda bana so inji mata ciwo."

Yace abin ya faru ne gidan yayar shi da take bangaren Ejigbo na jihar Legas.

Wanda ake zargi, inda lauyan shi Mista Worer Obuagbaka ya jagoranta yace hukumar yan sandan basu bashi damar magana ba kuma bai fada wa yan sandan cewa ya kwanta da ita ko a'a ba.

DUBA WANNAN: Cikakkun bayanai kan yadda tsohon gwamna ya kwan a kurkuku

"Wannan rahoton da kuke gani ba ni na rubuta shi ba, ba a bani wata takarda ba, wani mutum da ake kira Sean Paul yazo ya kaini inda IPO yake, abinda yayi na gaba shine mari na kuma naga sifeta Amina Adeoye da takarda wacce aka umarce ni da in sa hannu" Inji Okorie.

Da aka umarce ni da in karanto rahoton, Sean Paul ya naushe ni a kai,sai jini ya fara zuba inda na kasa karantowa. Sai kawai nasa hannu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel