‘Yan sara-suka 50 sun shiga hannu a jihar Kaduna bayan umarnin da El-Rufa’i ya bayar na a damko su

‘Yan sara-suka 50 sun shiga hannu a jihar Kaduna bayan umarnin da El-Rufa’i ya bayar na a damko su

- 'Yan sara-sukan da suka aikata barna makon da ya gabata sun fara shiga hannu

- Ya zuwa yanzu dai 50 sun shiga hannu har ma ana shirin kai su kotu

A kalla kimanin ‘yan kungiyar sara-suka 50 ne suka shiga hannun jami’an tsaro biyo bayan umarnin da gwamnan jihar Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ga jami’an tsaron domin su tabbatar da kawo karshen aikace-aikacen ‘yan kungiyar da suka addabi al’umma.

‘Yan sara-suka 50 sun shiga hannu a jihar Kaduna bayan umarnin da El-Rufa’i ya bayar na a damko su

‘Yan sara-suka 50 sun shiga hannu a jihar Kaduna bayan umarnin da El-Rufa’i ya bayar na a damko su

Wadanda ake zargin dai an kamo su ne daga wurare daban-daban daga suka hada da lungu da sako na jihar sakamakon wata hatsaniya da ta afku unguwar shanu makon da ya gabata.

KU KARANTA: Mutum 1 ya rasa ransa, an cafke 2 a wani rikici da ya barke a kaduna

Mai magana da yawun gwamnatin jihar ta Kaduna Samuel Aruwan ne ya shaida hakan ta cikin wani jawabi da aka fitar, inda ya tabbatar da cewa da zarar an kammala bincike za’a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Aruwan ya kuma kara da cewa, bayan bayanin da hukumomin tsaro na jihar suka gabatarwa gwamnan kan irin ta’adin da ‘yan kungiyar ta sara-suka suka tafka, gwamnan yayi ala-wadai da lamarin sannan ya ziyarci mutanen yankin Abakpa suka tattauna kan lamarin ‘yan sara-suka da matakin da zai dauka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel