Gwamnatin tarayya na daf da kara karbar $500m daga kudaden da Abacha ya wawura

Gwamnatin tarayya na daf da kara karbar $500m daga kudaden da Abacha ya wawura

- An rattaba hannu kan yarjejeniyar dawo wa Najeriya $500m daga kasashen Amurka, Faransa da Ingila

- Wadannan kudaden suna daga cikin kudaden da tsohon shugaban kasar Janar Sani Abacha ya wawure ya kai kasashen turai ne

- Ministan Shari'a na kasa, Malam Abubakar Malami ne ya bayar da sanarwan bayan ya fito daga taron FEC na wannan makon

An kammala taron majalisar zartarwa na kasa FEC da akayi a gidan gwamnati da ke Abuja cikin murna saboda labarin dawo wa Najeriya da zunzurutun kudi $500 miliyan daga kasashen Ingila, Amurka da Faransa cikin kudaden da tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kai ajiya a kasashen.

A yayin da ya ke sanar da manema labarau bayan taron, Attoney Janar kuma Ministan Shari'ah na kasa, Malam Abubakar Malami ya ce an cinma matsayar dawo da kudaden ne sakamakon tattaunawa da akayi tsakanin gwamnatin Najeriya da na kasashen uku.

Shugaba Buhari na tsammanin isowar wasu karin $500m daga kudaden da Abacha ya sakaya a kasashen Turai lokacin mulkin sa

Shugaba Buhari na tsammanin isowar wasu karin $500m daga kudaden da Abacha ya sakaya a kasashen Turai lokacin mulkin sa

KU KARANTA: Sojin ruwan Najeriya sunyi fata-fata da matatun man fetur 1000 da aka gina ba bisa ka'ida ba

A cewarsa, kudaden na zuwa ne jim kadan bayan kasar Switzerland ta dawo wa Najeriya da $322 daga cikin kudaden da Abacha ya sakaya a kasar ta Switzerland bayan Najeriya ta sa hannu kan wata yarjejeniya da Switzerland din.

Malami kuma ya amsa tambayoyi akan abinda kudin tsarin mulki ya ce game da canja ranar demokradiyya zuwa 12 ga watan Yuni tare da ayyana shi a matsayin ranar hutu da kuma bawa marigayi MKO Abiola da Cif Gani Fawehinmi da Ambasasada Baba Gana Kingibe lambar karramawa ta kasa.

Malami ya ce shugaban kasan yana da ikon bayar da lambar karramawar ba tare da tuntubar kowa ba. Ya kuma mayar da martani ga masu cewa ba dai-dai bane a bayar da lambar girmar da mutanr bayan sun mutu inda ya ce hakan ma ba gaskiya bane kuma ya bayar da misalin wata karramawa da akayi wa tsohon shugaban kasa Janar Murtala Mohammed bayan ya mutu.

Sai dai ya ce za'ayi wa kudin tsarin mulki kwaskwarima kafin a fara hutu a ranar 12 ga watan Yuni wanda shine ranar demokradiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel