Kada ku zabi bangare a zaben 2019 - Birtaniya ta Gargadi Hukumar EFCC

Kada ku zabi bangare a zaben 2019 - Birtaniya ta Gargadi Hukumar EFCC

Babban Jakadan Kasar Birtaniya zuwa Najeriya, Paul Arkwright, ya nemi hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa watau EFCC akan kada ta nuna wariya ko daukar wani bangare cikin jam'iyyun siyasa a yayin zaben kasa na 2019.

Arkwright ya kuma kirayi hukumar akan hada gwiwa da hukumar zabe ta kasa watau INEC wajen tabbatar da an gudanar da zaben ba tare da wata kwayar zarra ta Magudi ba.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Jakadan na kasar Birtaniya ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai shelkwatar Hukumar EFCC dake babban Birnin Kasar nan na Abuja a ranar Larabar da ta gabata.

Yake cewa, hukumomin INEC da EFCC su kasance sun yi tsayuwar daka ta kare mutunci na tsarin gudanar da siyasar Kasar nan ba tare da daukar wani bangare ba ko nuna wariya kan wata jam'iyya cikin jam'iyyun siyasa domin tabbatar da adalci.

Babban Jakadan Kasar Birtaniya zuwa Najeriya; Paul Arkwright

Babban Jakadan Kasar Birtaniya zuwa Najeriya; Paul Arkwright

Arkwright ya kuma bayar da tabbacin goyon bayan gwamnatin Kasar Birtaniya wajen bayar da taimako muhimmi a bangaren fasaha, bincike da kuma inganta harkokin gudanarwa na hukumar EFCC.

KARANTA KUMA: Hukumar FBI ta cafke Mutane 74 a Amurka, Najeriya da wasu Kasashe 3 bisa Laifin Zamba

Babban Jakadan ya kuma yabawa hukumar dangane da nasarorin ta na kwana-kwanan nan wajen tunkara da magance rashawa a Najeriya.

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu, ya yabawa gwamnatin kasar Birtaniya dangane da wannan goyon baya tare da bayar da tabbacin sa akan hukumar wajen sauke nauyin da rataya a wuyan ta.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Kasar Amurka tare da hadin gwiwar hukumar EFCC ta cafke wasu Mutane 29 'yan Najeriya da suka aikata laifin zamba kan wasu 'yan kasuwa na kasar ta Amurka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel