Miliyan N500m ta sanya wani tsohon minister da babban lauya shiga komar EFCC har sun kai su kotu

Miliyan N500m ta sanya wani tsohon minister da babban lauya shiga komar EFCC har sun kai su kotu

- A cigaba da yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa, EFCC tayi babban kamu

- Ta gurfanar da wani tsohon minista da kuma wani babban lauya mai lambar girma ta SAN

- EFCC dai na zarginsu da wata badakalar makudan kudade

Tsohon ministan tsare-tsare Farfesa Abubakar Sulaiman da kuma Dele Belgore (SAN) sun gurfana gaba wata babbar kotu a jihar Legas karkashin mai shari’a R.M Aikawa bisa zargin sama da fadi da makudan kudade har Naira miliyan N500m.

Miliyan N500m ta sanya wani tsohon minister da babban lauya shiga komar EFCC har sun kai su kotu

Miliyan N500m ta sanya wani tsohon minister da babban lauya shiga komar EFCC har sun kai su kotu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawan na zargin su biyun ne da hada baki gami da wawure kudaden a ranar 27 ga watan Maris 2015.

EFCC dai ta bayyana cewa wadanda take zargin sun biya wani mai suna Sheriff Shagaya zunzurutun kudade har Naira miliyan N450m da kuma karin wata Naira miliyan N50m a ranar 27 ga watan Maris 2015 ba tare da bin dokokin ka’idar ta’ammali da manyan kudade ba. A cewar EFCC wannan biyan kudi ya zarce adadin dokar kiyaye almundahanar kudade ta kasa.

KU KARANTA: Abubuwa 6 da ya kamata Musulmi ya sani kafin sallar Idi

“Wadanda muke kara (Farfesa Abubakar Sulaiman da kuma Dele Belgore ) tabbas su na da masaniyar cewa biyan irin wadannan kudade manya da suka kai N450m da N50m sabawa doka ne”. EFCC ta jaddada.

A bisa haka ne hukumar take zargin tsohon ministan da babban lauyan Dele Belgore (SAN) da aikata laifin da ya sabawa sashi 1(a), 16(d), 15(2)(d) and18(a) da take lura da ta’ammali da kudi ta 2012, saboda haka ne EFCC ke burin ganin an hukunta su bisa tanadin dokar sashi 15(3)(4), da 16(2)(b).

Miliyan N500m ta sanya wani tsohon minister da babban lauya shiga komar EFCC har sun kai su kotu

Miliyan N500m ta sanya wani tsohon minister da babban lauya shiga komar EFCC har sun kai su kotu

Amma sai dai wadanda ake karar sun ki amincewa da aikata laifi kwata-kwata. Wanda hakan ya sanya mai shari’ar ta bayar da su beli bisa karbar uzurin cewa duba da matsayinsu ba zasu tsere ba.

Amma kuma mai shari’ar yayi umarnin da a karbe Fasfo dinsu kuma kar a sake a bayar har sai kotun ce ta bayar da umarnin. Kana ya dage shari’ar zuwa zama na gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel