Sama da Mutane 10 sun gamu da ajalinsu a hannun yan bindiga a jihar Zamfara

Sama da Mutane 10 sun gamu da ajalinsu a hannun yan bindiga a jihar Zamfara

Rundunar Yansandan jihar Zamfara ta bayyana cewa mutane 10 sun mutu a sakamakon wani mummunan hari da wasu gungun yan bindiga suka kai a kauyen Dutsen Wake da kauyen Oho, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigar sun kai wannan hari ne a kauyukan biyu dake cikin karamar hukumar Birnin-Magaji, kamar yadda Kaakakin rundunar Yansandan jihar, DSP Muhammad Shehu ya tabbatar.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Kotu ta kwace naira biliyan 2.2 daga wajen wani babba a gwamnatin Jonathan

DSP Shehu yace wanan hari ya faru ne a ranar Talata, 14 ga watan Yuni da misalin karfe 10 na dare, amma nan da nan rundunar ta tura jami’anta zuwa kauyukan don fuskantar yan bindigan.

“Da isarsu kauyukan sai suka tarar har yan bindigan sun tsere zuwa dajin Rugu na jihar Katsina dake kan iyakar jihar Zamfara, inda suka gano gawar mutane 7 a kauyen Dutse Wake, 3 a kauyen Oho.” Inji DSP Shehu.

Daga karshe Kaakakin yace tuni kwamishinan Yansandan jihar tare da hadin gwiwar kwamishinan Yansandan jihar Katsina suka fara bin sawun yan bindigar don ganin an damko wuyansu, sa’annan ya bukaci al’ummomin jihar dasu taimaka musu da sahihan bayanai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel