Yanzu Yanzu: Buhari zai sanya hannu a kasafin kudin 2018 a mako mai zuwa - Adesina

Yanzu Yanzu: Buhari zai sanya hannu a kasafin kudin 2018 a mako mai zuwa - Adesina

Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman a kan shafukan zumunta da kafofin watsa labarai, Femi Adesina ya bayyana cewa shugaban kasar zai sanya hannu a kasafin kudin 2018 a mako mai zuwa.

Femi ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugabn kasa kan makomar taron bangaren zartarwa da aka gudanar a ranar Laraba, 13 ga watan Yuni, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa hadimin shugaban kasar ya sanar da manema labarai tare da ministan lafiya Farfesa Isaac AAdewole da kuma na kasuwanci da zuba jari, Okechukwu Enelamah.

Yanzu Yanzu: Buhari zai sanya hannu a kasafin kudin 2018 a mako mai zuwa - Adesina

Yanzu Yanzu: Buhari zai sanya hannu a kasafin kudin 2018 a mako mai zuwa - Adesina

A baya Legit.ng ta rahoto cewa fadar shugaban kasa ta tabbatar da risitin kasafin 2018 daga majalisar dokoki.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da wani mutum bayan yayi yunkurin yiwa mai ciki fyade

A halin da ake ciki Gwamnatin shugaban kasa Buhari na cigaba da farautan barayin gwamnati da ake zargi da wawure kudin kasa a lokacin da suke rike da kujerar mulki.

Hakan ya biyo bayan samun wata mai shari'a akan gaskiya da akayi, yanzu haka ta tura tsoffin gwamnoni biyu gidan yari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel