Kawar budurwa da ta jefa kanta ruwa ta kashe kanta tayi bayanin dalilan da suka sanya kawar kashe kanta
- A cewar majiyarmu, yarinyar ta kashe kanta ne saboda wai sharri da aka mata
- Ta ajje motarta ta jefa kanta ruwan Legas
- Hukumomi sun je neman gawarta a ruwa
A wani labari mai ban tausayi, an sami wata mata da ta jefa kanta ruwa a babbar gadar sama a jihar Legas, inda rahotanni suka ce ta rasu, har ma'aikatan LASTMA, suka basu aikin nemo gawarta.
Sai dai kawarta ta saki bayanai da cewa wai ai soyayya ce da ta hada ta da wani abokinta, inda bayan sun yi fada ta jefa kanta ruwa wai don gudun abin kunya.
DUBA WANNAN: Ya kashe wani don yayi kudi, kudin yaki zuwa
A cewar kawar, hotunan tsiraicin ta ne yayi yawo a wayoyin jama'a, wanda saurayinta ya yada don wanke kansa daga zargi, lamari wai da har ya kai ga maigidanta, lamari da ya kai ga ta ga babu wani abin yi banda tsunduma kanta ruwa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng