Cin hanci: Sakayyar shugaba Buhari ga Alkaliyar da ta kulle manyan Najeriya a kurkuku

Cin hanci: Sakayyar shugaba Buhari ga Alkaliyar da ta kulle manyan Najeriya a kurkuku

- Shugaba Buhari ya kyautata wa Justice Adebukola Banjoko

- A cewar majiyarmu, ya nada ta shugabantar kotun CCT

- Shi tsohon shugaban CCT yana fuskantar tuhuma

Cin hanci: Sakayyar shugaba Buhari ga Alkaliyar da ta kulle manyan Najeriya a kurkuku

Cin hanci: Sakayyar shugaba Buhari ga Alkaliyar da ta kulle manyan Najeriya a kurkuku

A sabbin bayanai da Legit.ng ke samu, Justice Adebukola Banjoko, Alkaliyar kotu da ta daure gwamnan jihar Pulato da na Taraba, shekaru akalla 14 a gidan yari, ta sami aikin shugabantar kotun CCT da ke bincikar manyan 'yan siyasa.

Aikin kotun shine tabbatar da an bada bayanai kan kadarori kafin da bayan anyi aiki a gwamnati, wanda ake sa rai 'yan siyasa zasu yi.

Kotun tayi kaurin suna lokacin shari'ar da ake yi wa Bukola Saraki daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

DUBA WANNAN: Ya kashe wani don yayi kudi, kudin yaki zuwa

Idan labarin ya tabbata, wannan ya nuna wasu 'yan siyasar da yawa zasu sake shiga hannu, musamman ganin ita bata wasa ko karbar cin hanci.

A baya dai, an zargi shugaban CCT din da karbar cin hanci da ya kai akalla $2m daga hannun Bukola Saraki, domin wanke shi daga zargin almundahana.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel