Shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2018 a makon gobe – Fadar shugaban kasa

Shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2018 a makon gobe – Fadar shugaban kasa

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mr Femi Adesina, ya bayyanawa manema labarai yadda ta wakana a taron majalisar zantarwa.

Ya ce shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2018 a mako mai zuwa wato bayan hutun Sallan Ramadana.

Da safe rahoton ya bayyana cewa shugaban kasa zai rattaba hannu kan kasafin kudin ne a yau amma hakan bai samu ba, bal shugaban kasa ya bada izinin gyaran wasu manyan hanyoyi ne a taron majalisan zantarwa da ya jagoranta a yau Laraba.

Shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2018 a makon gobe – Fadar shugaban kasa

Shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2018 a makon gobe – Fadar shugaban kasa

Hanyoyoin da za’a gyara sune Yobe, Adamawa, Benue, Kwara, Ekiti, Lagos, Ogun, Edo, Enugu, Borno, Anambra da Sokoto.

Hanyan Gwoza – Damboa – Goniri – Ngamdu a Yobe da Borno zai ci N34.608 billion; Mayo Belwa – Jada – Ganye – Torngo a jihar Adamawa zai ci N22.699billion; Ado – Ifaki – Otun – Kwara a jihar Ekiti zai ci N6 billion.

Ya ce za’a gyara gadan Makurdi a jihar Benue da kudi N4.617 billion; hanyan Ihugi – Korinya -Wuse -Ankor a Benue zai ciN15.641 billion; hanyan Gbagi – Apa – Owode a Badagry jihar Legas zai ciN4.366 billion.

Hanyan Ijebu Igbo – Ita Egba Owonowen a jihar Ogun zai ci N9.833 billion, sannan hanyan Jattu – Fugar – Agenebode a jihar Edo zai ci N7.506billion.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau, kalli hotunan

Hanyan Makurdi – Gboko – Wannune – Yander a jihar Benue zai ci N18.669 billion; hanyan Enugu – Port Harcourt a Agbogugu – Abia zai ci N13.933 billion.

Hanyan Umulungbe – Umoka; Amokwu – Ikedimkpe – Egede – Opeyi Awhum a jihar Enugu zai kwashi N21.729 billion; sannan hanyan Nkwu Inyi – Akpugoeze a jihar Anambra zai ci N2.595 billion.

A karshe, hanyan Sabon Birnin – Tsululu – Kuya – Maradi Junction a jihar Sokoto zai ci N4.354billion.

atsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel