Gwamnatin tarayya ta bada N185bn domin gyara manyan tituna 14 a fadin tarayya

Gwamnatin tarayya ta bada N185bn domin gyara manyan tituna 14 a fadin tarayya

Majalisar zantarwan tarayya a zamanta na yau ta bada izinin bayar da kudi N185.2billion domin gyaran hanyoyi 14 a fadin kasa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mr Femi Adesina, ya bayyanawa manema labarai yadda ta wakana a taron majalisar zantarwa.

Mr Adesina wanda ya yi bayanin tare da ministan sanya hannun jari, Okechukw Enalamah da ministan kiwon lafiya, Prof. Isaac Adewole ya ce hanyoyin da za’a gyara suna a Yobe, Adamawa, Benue, Kwara, Ekiti, Lagos, Ogun, Edo, Enugu, Borno, Anambra da Sokoto.

Hanyan Gwoza – Damboa – Goniri – Ngamdu a Yobe da Borno zai ci N34.608 billion; Mayo Belwa – Jada – Ganye – Torngo a jihar Adamawa zai ci N22.699billion; Ado – Ifaki – Otun – Kwara a jihar Ekiti zai ci N6 billion.

Ya ce za’a gyara gadan Makurdi a jihar Benue da kudi N4.617 billion; hanyan Ihugi – Korinya -Wuse -Ankor a Benue zai ciN15.641 billion; hanyan Gbagi – Apa – Owode a Badagry jihar Legas zai ciN4.366 billion.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau, kalli hotunan

Hanyan Ijebu Igbo – Ita Egba Owonowen a jihar Ogun zai ci N9.833 billion, sannan hanyan Jattu – Fugar – Agenebode a jihar Edo zai ci N7.506billion.

Hanyan Makurdi – Gboko – Wannune – Yander a jihar Benue zai ci N18.669 billion; hanyan Enugu – Port Harcourt a Agbogugu – Abia zai ci N13.933 billion.

Hanyan Umulungbe – Umoka; Amokwu – Ikedimkpe – Egede – Opeyi Awhum a jihar Enugu zai kwashi N21.729 billion; sannan hanyan Nkwu Inyi – Akpugoeze a jihar Anambra zai ci N2.595 billion.

A karshe, hanyan Sabon Birnin – Tsululu – Kuya – Maradi Junction a jihar Sokoto zai ci N4.354billion.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel