An gurfanar da wani mutum bayan yayi yunkurin yiwa mai ciki fyade

An gurfanar da wani mutum bayan yayi yunkurin yiwa mai ciki fyade

Wata kotun majistare na Osun dake zama a Modakeke, Ile-Ife ta gurfnar wani Emmanuel Ademakinwa mai shekaru 29 kan yunkurin yiwa mai ciki fyade.

Mai shari’a, Misis A.O. Famuyide taki ba da belin wanda ake zargin sannan kuma tayi umurnin tsare shi a kurkukun Ile-Ife.

Famuyide ta dage shari’an zuwa ranar 28 ga watan Yuni.

Inspecta Ona Glory ya fadama kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin a ranar 7 ga watan Yuni, da misalin 1.00 na dare a Modakeke, karamar hukumar Ife North-East dake Osun.

An gurfanar da wani mutum bayan yayi yunkurin yiwa mai ciki fyade

An gurfanar da wani mutum bayan yayi yunkurin yiwa mai ciki fyade
Source: Twitter

Glory ya bayyana cewa wanda ake zargin yaci zarafin matar mai cikiyar shekara 21 ta hanyar kwantawa akan ta da kudirin Tarawa da ita ba tare da amincewarta ba.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyarmu na sauya rayuwar yan Najeriya, sauran jam’iyyu duk wasa suke – Jigon APC

Ya kara da cewa mai laifin ya kuma sace kudin mai karafin N45, 000 wanda ta ajiye a cikin Jakarta a dakin.

Wanda ake zargin ya amsa laifin yunkurin lalata da ita amma ya karyata cewan yayi mata sata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel