Wani tsohon gwamna ya fice daga jam'iyyar PDP

Wani tsohon gwamna ya fice daga jam'iyyar PDP

Tsohon gwamnan jihar Ondo, Dakta Olsegun Mimiko ya aike wa mahukuntar jam'iyyar PDP da wasikar ficewa daga jam'iyyar bayan ya kammala shirin komawa jam'iyyar sa ta da wato Labour Party.

An gano cewa tsohon gwamnan wanda ya shiga PDP a 2014 kuma daga baya za zama shugaban gwamnonin jam'iyyar ya yanke shawarar barin jam'iyyar ne saboda wata rashin jituwa da ta faru tsakanin sa da wasu shugabanin jam'iyyar na kasa jim kadan bayan saukarsa daga kujerar gwamna a 2017.

A wasikar da ya aike zuwa ga shugaban jami'iyyar a yau Laraba, Mimiko ya bai fayyace dalilin da yasa ya fice daga jam'iyyar ba inda ya ce ba dalilan da zai iya bayyanawa duniya bane.

Wani tsohon gwamna ya fice daga jam'iyyar PDP

Wani tsohon gwamna ya fice daga jam'iyyar PDP

KU KARANTA: Abubuwan da muka tattauna jiya a taron da mu kayi da Buhari - Okorocha

Wani sashi na wasikar ya ce, "Ina amfani da wannan damar don in sanar da kai niyya ta na ficewa daga jam'iyyar PDP daga ranar 13 ga watan Yuni 2018 saboda wasu dalilai na kashin kai na."

Nayi matukar godiya saboda alfarmar da na samu na yin aiki da wasu manyan Najeriya a jam'iyyar PDP a lokacin da nake mamban jam'iyyar.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa Mimiko yana zai koma jam'iyyar da ya baro ta Labour Party a kauyensu da ke jihar Ondo sai dai mafi yawancin magoya bayansa za suna nan a jam'iyyar ta PDP

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel