Yaki da Rashawa: Ingila za ta hana barayin gwamnatin Najeriya guduwa su buya a kasarta

Yaki da Rashawa: Ingila za ta hana barayin gwamnatin Najeriya guduwa su buya a kasarta

- Manyan yan Najeriya da ake tuhuma da satar kudaden al'umma za su shuga uku mai wuya saboda kasar Ingila tana gab da haramta musu shigowa kasar ta

- Kasar Amurka ne ta fara daukan wannan matakin da fara janye izinin shiga kasar Amurka na Cif Raymond Dokpesi

- Wata kwamiti na musamman ta fara hadin gwiwa da sakaten gida na kasar Ingila

Bayan kasar Amurka ta haramtawa Cif Raymond Dokpesi izinin shiga kasar ta, Kasar Ingila itama tana tunanin daukan mataki mai kama da hakan na haramtawa 'yan Najeriya musamman wadanda suka rike mukamman gwamnati da ke fusknatar tuhumar almundahana neman buya a kasar.

Yaki da Rashawa: Ingila zata hana barayin gwamnatin Najeriya guduwa su buya a kasarta

Yaki da Rashawa: Ingila zata hana barayin gwamnatin Najeriya guduwa su buya a kasarta

Shugaban kwamitin bincike na musamman (SPIP), Okoi Obono-Obla ya fitar da sanarwa a ranar Laraba 13 ga watan Yuni inda ya ce SPIP tana hadin gwiwa da ofishin sakataren harkokin gida na Ingila.

KU KARANTA: Ka shiga taitayin ka - APC ta ja kunnen wani gwamnan ta

Obono-Obla ya ce ana hadin gwiwan ne don tabbatar da cewa wasu da suka rike manyan mukaman gwamnati da ake zargin sun saci kudin al'umma sun sayi kadarori a Najeriya da Ingila basu samu daman buya a kasar ba kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Legit.ng ta gano cewa ciyaman din kwamitin ya ce: "Kwamitin ta tattaro sunayen mutane sama da 200 ciki har da wanda su kayi rike mukamman gwamnati a baya da wanda ke rike dashi yanzu da ake zargin sun handami kudin al'umma sun azirta kansu."

A cewarsa, kwamitin ta gano wata haramtaciyyar $7 miliyan da aka ajiye a Bankin Heritage. Ya ce ana cigaba da gudanar da bincike a kan wasu tsaffin gwamnoni da yan majalisa a halin yanzu.

Legit.ng kuma ta ruwaito labari inda kasar Amurka ta karbe takardan izinin shiga kasar ta daga hannun wani dan jam'iyyar PDP Cif Raymond Dokpesi saboda sunansa na cikin jerin sunayen wanda ake zargi da satan kudin al'umma da gwamnatin tarayya ta fitar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel