Yadda Shema ya yi sama da fadi akan kudaden kananan hukumomi – Mai shaida

Yadda Shema ya yi sama da fadi akan kudaden kananan hukumomi – Mai shaida

Wani mai bayar da shaida a cigaba da shari’ar tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema, da ake yi ya bayyana yadda tsohon gwamnan ya rattaba hannu inda ya yarda a kashe kudaden kananan hukumomin jihar a tsakanin 2013 da 2015, ba tare da bin ka’idar da doka ta gindaya ba.

Ibrahim Bujawa ne ya yi wannan cikakken bayani ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa sannan kuma aka gabatar da kwafin bayanin nasa a gaban kotu, a matsayin shaida mai lamba 2.

Mai bayar da shaidan, ya bayyana cewa kungiayar da aka kafa don ta binciki yadda aka kashe kudaden, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin, sun gano cewa an bi wasu hanyoyi aka yi asarkala da kudaden.

Yadda Shema ya yi sama da fadi akan kudaden kananan hukumomi – Mai shaida

Yadda Shema ya yi sama da fadi akan kudaden kananan hukumomi – Mai shaida

Ya cigaba da cewa mafi akasarin kudaden ana ta karkata su ko kuma an rika fitar da su ne zuwa ga asusun Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Jiha (ALGON), wadda kungiya ce kawai ba hukuma ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni 7, Tinubu da Akande sun tsayar da Oshiomhole

Daga nan sai alkali Bako ya dage sauraron karar zuwa ranar 9 da 10 ga watan Yuli, domin a zartar da hukunci akan shaidar. Daga nan kuma za a ci gaba da shari’a.

Ana dai gurfanar da Shema ne tare da wasu mutane uku, Ibrahim Lawal Dankaba, Sani Hamisu Makana da kuma Ahmed Rufai Safana bisa tuhumarsu da ake yi da yin kundunbala da makudan kudade har naira biliyan 11 daga cikin kudaden asusun ajiyar kananan hukumomin jihar Katsina.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Za ku iya samun a: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel