Yanzu-yanzu: Kotu ta salami wani sanatan PDP

Yanzu-yanzu: Kotu ta salami wani sanatan PDP

Wata babban kotun tarayya da ke zaune a Abuja ta yanke hukuncin sallaman sanata Atai Aidoko, mai wakiltar Kogi ta yamma daga majalisan dattawa.

Kotun karkashin jagorancin alkali mai shari’a, Jastis Kolawale Gabriel ya yanke hukuncin cewa an baiwa Mr Aidoko kujeran takara karkashin jam’iyyar PDP ne bisa ga kuskure a zaben fidda gwanin da sukayia a watan Disamban 2014.

Ainihin wanda ya lashe zaben, Isaac Alfa, ya kai kara kotu domin kwato masa hakkinsa tun lokcain da aka gudanar da zabe.

Yanzu-yanzu: Kotu ta salami wani sanatan PDP

Yanzu-yanzu: Kotu ta salami wani sanatan PDP

Duk da cewa kotun daukaka kara ta bada umurni a koma kotu domin baiwa mai hakki hakkinsa, Mr Aidoko ya rantse ba zai fita daga majalisa ba kuma ya cigaba da halartan zaman majalisa.

Amma a yau Laraba, kotu ta umurci jam’iyyar PDP da Mr Aidoko su biya Mr Alfa diyya N750,000 kowannensu.

Ku saurari cikakken rahoton…

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel