Kasar Spain ta kori Kocin ta a Jajiberin Gasar cin Kofin Duniya

Kasar Spain ta kori Kocin ta a Jajiberin Gasar cin Kofin Duniya

Da sanadin kafofin watsa labarai na wasanni mun samu rahoton cewa, Kasar Andalus watau Spain ta sallami Kocin ta Julen Lopetegui, a ranar yau ta Laraba da ta yi daidai da jajiberin gasar cin kofa Duniya da za'a fara karawa a gobe Alhamis.

Hukumar kwallon kafa ta Kasar ta Spain ta sallami Lopetegui ne sakamakon amincewar sa na karbar aikin horar da 'yan wasa na Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da zarar an kammala gasar kofin na Duniya.

A ranar Talatar da ta gabata ne rahotanni suka yadu na cewar Julen ya aminta da karbar ragamar Kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid inda zai dirfafi aiki da zarar an kammala gasar kofin Duniya.

Kocin da Kasar Spain ta kora; Julen Lopetegui

Kocin da Kasar Spain ta kora; Julen Lopetegui

Wannan rahoto da hukumar kwallon kafa ta Spain ta yi kacibus da shi 'yan dakikai kadan kafin yaduwar sa a duniya ya sanya ta fusata wajen yanke wannan hukunci kan Kocin da a da zai jagoranci kasar ta zuwa gasar Kofin Duniya.

KARANTA KUMA: Amurka, Kanada da Mexico za su karɓi bakuncin Gasar cin Kofin Duniya 2026

Kamar yadda ta bayyana a shafin ta na yanar gizo, a halin yanzu tuni kasar ta mika wannan ragamar a hannun wani tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar, Fernando Hiero, wanda daman yana rike da wani mukami a cikin hukumar kwallon Kafa ta Spain.

Sabon Kocin Kasar Spain; Fernando Hiero

Sabon Kocin Kasar Spain; Fernando Hiero

Legit.ng ta fahimci cewa, Lopetegui ya amince da karbar aikin kungiyar Reak Madrid da ta lashe gasar kofin zakarun Turai yayin da mai horar da 'yan wasa, Zinedine Zidane ya yi murabus a watan Mayun da ya gabata.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Kasar Amurka ta yo takakka ta yashe wasu 'yan Najeriya 29 da suka aikata laifin zamba na wawushe dukiyar wasu Al'ummar kasar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel