Wata motar alfarma ta kutsa cikin wani masallaci bayan ta kwace daga hannun direba, duba hotuna

Wata motar alfarma ta kutsa cikin wani masallaci bayan ta kwace daga hannun direba, duba hotuna

Jami’an bayar da agajin gaggawa a jihar Legas (LASEMA) sun yi nasarar zaro wata mota da ta kutsa cikin wani masallaci a unguwar Isolo bayan kwacewa daga hannun direban ta.

Babu rahoton rasa rai ko samun raunuka sakamakon afkuwar hatsarin. Kazalika majiyar mu bata bayyana ma ma ko direban motar ya samu rauni ba.

Ko a kwanakin saida jami’an bayar da agajin suka shiga kokarin gano mamallakin wata motar alfarma da ya bar ta a tsakiyar titi sannan ya yi allan-baku cikin tekun kasan gadar Third Mainland.

Wata motar alfarma ta kutsa cikin wani masallaci bayan ta kwace daga hannun direba, duba hotuna

Wata motar alfarma ta kutsa cikin wani masallaci bayan ta kwace daga hannun direba

Wata motar alfarma ta kutsa cikin wani masallaci bayan ta kwace daga hannun direba, duba hotuna

Jami'an LASEMA na kokarin fitar da motar daga masallaci

Wata motar alfarma ta kutsa cikin wani masallaci bayan ta kwace daga hannun direba, duba hotuna

Wata motar alfarma ta kutsa cikin wani masallaci bayan ta kwace daga hannun direba

Ya bar motar ta sa kirar Ford Explorer ta miliyoyi dake da lambar mallaka APP 190CE a saman gadar da ba ya rabuwa da gudanarwar ababen hawa.

DUBA WANNAN: Na shiga sana'ar garkuwa da mutane domin samun kudin hidimar sallah - Wani matashi

LASEMA na kokarin binciko dalilin da ya saka mutumin aikata hakan duk da sun yi amanna cewar ya kashe kan sa ne.

LASEMA ta ce tana kokarin tabbatar da maganganun da shaidun gani da ido suka fada masu dangane da fadawar mutumin cikin tekun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel