Ba laifi bane koda ace saboda 2019 Buhari ya karrama Abiola – Balarabe Musa

Ba laifi bane koda ace saboda 2019 Buhari ya karrama Abiola – Balarabe Musa

A ranar Talata, 12 ga watan Yuni tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa yace ba laifi bane koda ace saboda neman kujerar shugabancin kasa a zabe mai zuwa ne ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari karrama marigayi Basorun MKO Abiola, wanda yayi nasarar lashe zabe a ranar 12 ga wayan Yunin 1993.

Ku tuna cewa a makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya sanar da 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Dimokradiyya sannan kuma ya karrama marigayi Abiola da matsayi mafi girma.

Wasu yan Najeriya sun yi has ashen cewa shugaban kasar yayi wannan yunkuri ne kawai domin ganin ya samu kuri’u yankin Yarbawa a zaben 2019.

Sai dai Musa yace koda saboda hakan Buhari ya karrama Abiola, thya cancanci yabo saboda yayi abunda ya kamata sannan ya gyara kuskuren da akayi a baya.

Ba laifi bane koda ace saboda 2019 Buhari ya karrama Abiola – Balarabe Musa

Ba laifi bane koda ace saboda 2019 Buhari ya karrama Abiola – Balarabe Musa

A bangare guda, Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnonin jam’iyya mai mulki wato APC guda bakwai, tare da babban jigon jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da kuma shugaban jam’iyyar na farko, Cif Bisi Akande sun kai ziyarar bangirma ga ofishin yakin neman zaben Adams Oshiomhole, dan takarar shugabancin jam’iyyar dake kan gaba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni 7, Tinubu da Akande sun tsayar da Oshiomhole

Gwamnonin da Oshiomhole ya jagoranta domin zaga ofishin yakin neman zaben sun hada da included Atiku Bagudu, Kebbi; Ibikunle Amosun, Ogun; Rotimi Akeredolu, Ondo; Umar Ganduje, Kano; Tanko Al-Makura, Nasarawa; Simon Lalong, Plateau; da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin samun ingantattun labarai, bide mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel