Tsohon Gwamna da aka yanke masa shekaru 14 a gidan Yari yace duk yan Najeriya barayi ne

Tsohon Gwamna da aka yanke masa shekaru 14 a gidan Yari yace duk yan Najeriya barayi ne

A yanzu dai a iya cewa ruwa ya kare ma dan kada, tunda har tsohon gwamnan jihar Filato, kuma Sanata mai wakiltar al’ummar jihar a majalisar dattawa, Joshua Dariye ya fara borin kunya, yana shure shure wanda bata hana mutuwa.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Talata, 12 ga watan Yuni ne wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Abuja ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawo shekaru 16 sakamakon kama shi da tayi da karkatar da makudan kudi naira biliyan 1.6 daga batil malin jihar Filato.

KU KARANTA: Tsautsayi baya wuce ranarsa: Wani katafaren gini ya ruguzo akan wasu Leburori 4

Sai dai rahotanni sun nuna cewa a lokacin da lauyan hukumar EFCC, Rotimi Jacobs ke bukatar Kotu ta tabbatar da kwakkwaran hukunci akan tsohon gwamnan don hakan ya zama izina ga na baya, sai tsohon gwamnan ya nemi yayi jawabi a gaban Kotu, inda Alkalin Kotun Adebukola Banjoko ya bashi dama.

A jawabinsa, tsohon gwamnan ya tambayi lauyan EFCC, Jacobs ya fada masa mutum guda daya a Najeriya dake da gaskiya, wanda barawo ba; “Ba ka san abinda ke cikin raina ba a yanzu, bai kamata mu bata yau saboda gobe ba, zaka iya rantsewa akwai mutumin kirki a Najeriya?

Sai dai lauyan EFCC y adage kai da fata cewa lallai Kotu ta zartar da hukunci mai tsauri akan Dariye, musamman duba da cewar bai nuna wani alamun damuwa ba da laifin da ya aikata, wanda kuma hakan aka yi, ya gamu da hukuncin shekaru 14 a gidan Yari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel