Hukumar FBI ta cafke Mutane 74 a Amurka, Najeriya da wasu Kasashe 3 bisa Laifin Zamba

Hukumar FBI ta cafke Mutane 74 a Amurka, Najeriya da wasu Kasashe 3 bisa Laifin Zamba

Ma'aikatar Shari'a ta kasar Amurka ta bayar da sanarwar cafke mutane 74 a 'yan Amurka da wasu 'yan kasashen ketare da suka hadar da mutane 29 na Najeriya da kuma mutane uku daga kasashen Kanada, Mauritius da kuma Poland.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana an cafke wannan adadi na mutane sakamakon aikata laifi na zambar dukiya ta wasu al'umma a kasar ta Amurka.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan mutane sun shiga hannu bisa aikata laifin wawushe dukiyar wasu al'umma musamman manyan ma'aikatan kasar Amurka ta hanyar zamba wajen amfani da tashoshi da hanyoyin sadarwa na shafukan yanar gizo.

Ma'aikatar Shari'ar ta bayyana cewa, a sakamakon hadin gwiwar bincike na tsawon watanni shidda da wasu hukumomin tsaro na kasar suka gudanar ya sanya aka bankado wannan miyagun mutane tare da kai cafka a gare su.

Legit.ng ta fahimci cewa, a sakamakon wannan bincike hukumomin sun kuma samu nasarar kwato makudan dukiya daga hannun mazambatan ta kimanin Dalar Amurka Miliyan 16.2 da suka yashe na al'umma.

Hukumar FBI ta cafke Mutane 74 a Amurka, Najeriya da wasu Kasashe 3 bisa Laifin Zamba

Hukumar FBI ta cafke Mutane 74 a Amurka, Najeriya da wasu Kasashe 3 bisa Laifin Zamba

Binciken ya tabbatar da yadda mazambatan ke yashe kudaden al'ummar Kasar Amurka dake gudanar da harkokin kasuwancin su ta yanar gizo a yayin shige da fice na dukiya sakamakon yadda ci gaba na ilimin fasahar zamani ya tanadar.

Ma'aikatar ta kara da cewa, binciken ya kuma bankado yadda wannan kungiya ta mazambata ta samo asali da tushe a Kasar Najeriya inda ta yadu zuwa sassa daban-daban a fadin Duniya.

KARANTA KUMA: Jerin Sanannun 'Kasashe 9 masu Makaman Nukiliya a Duniya

Christopher Wray, Shugaban hukumar tsaro ta bincike na kasar Amurka watau FBI (Federal Bureau of Investigation) ya bayyana cewa, wannan kwazo da hukumomin tsaro suka aiwatar shi ya tabbatar da sadaukar da kai ga tarwatsa gami da dakile duk wata gudanarwa ta miyagu dake nufin rusa 'yan kasar Amurka da harkokin su na kasuwanci.

Hakazalika Lauyan Kolu na kasar Amurka, Jeff Sessions, ya yabawa wannan kwazo na hukumomin tsaro da kasashen da wannan lamari ya shafa gami da hukumomin masu hana yiwa tattalin arziki zago kasa musamman ta EFCC da bayar da hadin kai wajen wannan gagarumar nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel