Ka shiga taitayin ka - APC ta ja kunnen wani gwamnan ta

Ka shiga taitayin ka - APC ta ja kunnen wani gwamnan ta

Mahukuntan jam'iyyar APC sunyi gargadi ga gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo bisa suka da ya keyi a kan jam'iyyar inda suka ce abinda ya dace ga wanda ya fada rami shine ya dena hakka don gujewa kara dilmiyewa.

A wata gargadi mai zafi da jam'iyyar ta fitar ta bakin sakataren ta, Mallam Bolaji Abdullahi a yau Laraba, ya ce gargadin ya biyo bayan wasu kallamai da gwamnan ya danganta a kan shugabancin jam'iyyar.

Ka shiga taitayin ka - APC ta ja kunnen wani gwamnan ta

Ka shiga taitayin ka - APC ta ja kunnen wani gwamnan ta

Idan ba'a manta ba cikin makonin da suka shude, "Okorocha ya yi ta fadin maganganu da babu gaskiya cikinsu game da shugabanin jam'iyyar mu. A kusan kullum sai gwamna Okorocha ya bude baki ya soki ciyaman din jam'iyyar su na kasa, Cif John Odigie-Oyegun da sauran shugabanin jam'iyyar a kan zabukan mahukunta jam'iyyar da akayi a Jihar Imo."

KU KARANTA: Kan 'yan majalisa ya rabu a kan dambaruwar dake faruwa tsakanin Buhari da Obasanjo

Jam'iyyar ta ce a wata rubutu da aka wallafa a jarida mai taken; "A bar gaskiya tayi halinta" wanda wani hadimin gwamna Okorocha mai suna Hon. Ireagwu Obioma ya sanya hannu a kai dauke da karairayi a kan jam'iyyar.

Duk dai a cikin rubutun da aka wallafa, hadimin Okorocha ya yi ikirarin cewa jam'iyyar APC tana da masaniya a kan umurnin kotu na dakatar da gudanar da zabbukan mahukunta jam'iyyar da akayi a jihar.

Sai dai jam'iyyar ta APC tace takardan kotun da aka wallafa a jaridar ta nuna cewa an aike wa jam'iyyar takardan ne a ranar 18 ga watan Mayun 2018 yayinda shi kuma zabukan mahukunta jam'iyyar na kananan hukumomi anyi shi ne a ranar 5 zuwa 14 ga watan Mayu wanda hakan ke nuna cewa sai bayan taron ne aka aike da takardan kotun.

Jam'iyyar dai ta sake jan kunne ga gwamna Okorocha ya dena irin sukar da yake yiwa shugabanin jam'iyyar, ya bi hanyoyin sulhu ta shigar da kara da jam'iyyar ta shimfida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel