Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau, kalli hotunan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau, kalli hotunan

- Har yanzu Buhari bai nada sabon ministan ma'adinai ba bayan Fayemi ya yi murabus

- Fayemi ya yi murabus ne domin takarar kujeran gwamnan jihar Ekiti da za'a gudanar a watan gobe

Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa tarayya a yau Laraba, 13 ga watan Yuni 2018 a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa, babban birnin tarayya Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci taron majalisar sune mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo, ministan kudi, Kemi Adeosun; ministan birnin tarayya, Muhammad Bello; karamin ministan ruwa, Bwari, ministan shari'a. Abubakar Malami.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau, kalli hotunan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau, kalli hotunan

Sauran sune ministan aikin noma, Audu Ogbeh; babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Babagana Munguno; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan gwamnati, Oyo Ita.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau, kalli hotunan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau, kalli hotunan

Majalisar zantarwa tarayya ta kunshi dukkan ministocin gwamnati, manyan masu baiwa shugaban kasa shawara, masu magana da yawunsa, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, shugaban ma’aikatan gwamnati, sakataren gwamnatin tarayya da kuma duk wani mai fada aji a fadar shugaban kasa.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau, kalli hotunan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau, kalli hotunan

Ana wannan ganawa ne kowani mako domin tattauna yadda abubuwa ke gudana a ma'aikatun gwamnatin da kowani minista ke jagoranta da kuma abubuwan da ke faruwa a fadin kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel