Hukumar kwastam ta yi ram manyan motoci 15 da kwantena 4

Hukumar kwastam ta yi ram manyan motoci 15 da kwantena 4

Hukumar kwastam na Najeriya shiyar jihar Legas a yau Laraba ta yi ram kwantena 4 jibge da kayayyaki kan laifan karya da masu kwantenan sukayi na kayayyakin da ke ciki.

Shugaban shiyar, Mohammed Ubam ya ce 2 daga cikin kwantenonin na dauke da silinda 8,633 sabanin kayan aikin famfo da masu shi sukayi ikirari. Yayinda sauran biyun kuma na dauke da jakunnan kaya 120 sabanin inji da akayi ikirari.

Kwantenonin masu lamba PCIU850134/9, PCIU8278544, FCIU983753, da TGHU6924330 sun shigo ne ta tashoshin jirgin ruwa daban-daban a jihar Legas.

Kana hukumar ta yi babban kamu tsakanin ranan 16 ga watan Mayu da 12 ga watan Yuni, daga cikin abubuwan da suka kama shine motoci kirar Toyota C-HR (2018) guda 3, Toyota Camry LE (2018) guda 1, Toyota Prado (2018) guda 1, Toyota Hilux (2017) guda 1, Ford F150 (2017) guda 1, Pajero Jeep (2017) guda 1, da Mercedes Benz (2017) 1.

KU KARANTA: Ba ni kadai ba ne barawo a Najeriya, yan siyasa ne manyan barayi amma ba’a musu komai – Barawon Keke Napep

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Hukumar Kastam ta hana fasakauri ta bayyana a ranar cewa, cikin sauke nauyin da rataya a wuyanta ta yi nasarar datse haramtattun buhunan shinkafa 1, 500 da kuma man gyada na kimanin Naira miliyan 65 a jihar Kaduna.

Shugaban wannan reshe, Kwanturola Usman Dakingari shine ya bayyana hakan a yayin gabatarwa manema labarai kayan fasakaurin da suka dakile cikin wasu tireloli biyu da aka yi basaja da su ta danyar gyada da kuma citta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel