Jam'iyyar mu ta APC na daf da mutuwa - Inji wani Sanata

Jam'iyyar mu ta APC na daf da mutuwa - Inji wani Sanata

Sanannen Sanatan nan dake wakiltar al'ummar mazabar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattijai Sanata Dino Melaye ya kwatanta jam'iyyar su ta APC mai mulki da mutumin da bai lafiya, magashiyyan.

Sanata Dino ya bayyana hakan ne a lokacin da ake fira da shi a gidan Talabijin din nan mai zaman kan sa na Channels a cikin shirin 'Siyasar mu a Yau'.

Jam'iyyar mu ta APC na daf da mutuwa - Inji wani Sanata

Jam'iyyar mu ta APC na daf da mutuwa - Inji wani Sanata

KU KARANTA: Tsaffin gwamnoni 4 da aka taba rufewa a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa Sanatan ya kuma kara da cewa shi babban abunda ke damun sa ma shine yadda jam'iyyar ke ta kara yin nisa da zukatan talakawan kasar a kullum.

A wani labarin kuma, Jigo a jam'iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan jihar Edo dake a kudu-maso-kudancin Najeriya Kwamarade Adams Oshiomhole a jiya ya bayyana cewa da shi ne shugaba Buhari da tuni tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo yana gidan yari.

Tsohon gwamnan dai wanda yanzu haka yake neman takarar zama shugaban jam'iyyar APC na kasa yayi wannan kalaman ne a lokacin da ya samu tubarrakin daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar Cif Bola Tinubu da kuma gwamnonin jam'iyyar game da kudurin sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel