Bukukuwan Sallah: Za'a baza jami'an 'yan sanda 3,500 don bayar da kariya ga al'ummar jihar Buhari

Bukukuwan Sallah: Za'a baza jami'an 'yan sanda 3,500 don bayar da kariya ga al'ummar jihar Buhari

Jami'an tsaron rundunar 'yan sanda a jihar Katsina ta sanar da cewa ta shirya tsaf domin baza mutanen ta akalla dubu 3 da 500 a dukkan lungu da sakon jihar domin tabbatar da bayar da tsaro ga al'umma a yayin bukukuwan Sallah karama da ke tafe.

Wannan dai kamar yadda muka samu, na a matsayin kari ne ga wasu jami'an tsaron farin kaya watau Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) 500 da sojoji da ma wasu jami'an tsaron na daban da za'a kara bazawa a jihar.

Bukukuwan Sallah: Za'a baza jami'an 'yan sanda 3,500 don bayar da kariya ga al'ummar jihar Buhari

Bukukuwan Sallah: Za'a baza jami'an 'yan sanda 3,500 don bayar da kariya ga al'ummar jihar Buhari

KU KARANTA: Wani dan Najeriya ya bizne mahaifin sa a mota

Legit.ng ta samu cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar a jihar ta Katsina DSP Gambo Isa ne ya sanarwa da manema labarai hakan a ofishin sa.

A wani labarin kuma, Alkaliyar wata kotun tarayya dake zaman ta a garin Kano mai suna Mai shari'a Zainab Bage Abubakar ta haramtawa tsohon gwamnan jihar Kano, Alhaji Ibrahim Shekarau zuwa kasar Saudiyya don yi Umarah ta hanyar kin bashi fasfo din sa.

Tun farko dai, tsohon gwamnan na jihar Kano ya roki kotun ce da ta dubi girman Allah ta bashi fasfo din sa tun a ranar 28 ga watan Mayun da ya gabata domun ya samu damar zuwa yayi ibada a kasa mai tsarkin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel